An bayyana cewa haka ta cimma ruwa a kokarin neman danyen man fetur da ake yi, domin Ministan Fetur, Timiprey Silva ya ce an samu danyen mai kwance karkashin kasa kimanin ganga bilyan 1 a yankin Arewa maso Gabas.
Sylva ya yi wannan furuci ne a wurin rufe taron sanin makamar aiki kan harkokin fetur a Abuja a ranar Laraba.
“Har yanzu masu binciken hako mai ba su kammala gano takamaimen adadin ba. Amma dai duban farkon farkon da aka yi ya nuna akwai kimanin gangar danyen mai bilyan 1 a karkashin kasa a yankin Arewa maso Gabas.
Sylva ya ce alamomi na kara nuna ba wannan ne kadai danyen mai da ke kwance a karkashin kasa a yankin Arewa maso Gabas ba.
Ya ce idan aka ci gaba da tonawa da hakawa, za a binciko fetur mai yawan gaske a yankin.
Da ya ke magana kan arzikin danyen mai a Najeriya, ya ce, ” bari na ba ku wani misali, a 2002 Najeriya na da kiyasin ganga bilyan 22 ta danyen mai. Amma an yi nasarar kara ta zuwa ganga bilyan 37 ya zuwa shekarar 2007.
“Amma daga 2007 zuwa yau, ganga milyan 500 kadai aka samu kari. Ba a ma kara daga bilyan 37 zuwa bilyan 38 ba. Saboda me? Saboda babu manyan masu shigowa su na zuba jari a Najeriya.”
Dalili kenan ya ce ya na sa ran Majalisar Dattawa da Majalisar Tarayya za su hanzarta sa hannu a kan Kudirin Dokar Man Fetur, wanda ake ta kai ruwa rana a tsawon shekaru a na so ya zama doka.
Ya kuma ce ba da dadewa ba za a fara aikin gyara matatar mai ta Fatakwal, wadda ita ce mafi girma a kasar nan.
Daga nan kuma inji shi za a duba matatar Warri da ta Kaduna a kara nazarin yadda za a kamo na su aikin gyaran.