An damke wanda yayi lalata da yara maza 6 ta dubura

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Anambra ta damke wani mutum dake yin lalata da yara maza ta dubura a Awka.

Kakakin ‘yan sandan jihar, Haruna Mohammed ya bayyana cewa mai laifi ya amsa laifinsa da kansa sai dai ya nemi ayi masa sassauci, cewa hudubar shaidan ya bi.

Shi dai wannan mutum mai suna Emmanuel Bassey ya kan danne yaran da basu wuce shekaru 10 zuwa 14 ne yayi lalata da su ta dubura.

Haruna ya ce da zaran ‘yan sanda sun gama bincike akai zasu maka shi a kotu.

Bayannan rundunar ta ceto wata yar shekara 10 da ala satota daga iyayen ta aka saida wa wasu iyayen akan naira 800,000.

Share.

game da Author