Abin da ya sa za mu sake ciwo wani bashin dala bilyan 22.8 -Gwamnatin Tarayya

0

Gwamnatin Tarayya ta nemi amincewar Majalisar Dattawa domin sake ciwo wani bashi har na dala bilyan 22.8.

Ministar Harkokin Kudade, Zainab Ahmed ce ta gabatar da wannan roko a gaban Kwamitin Lura da Basussuka na Cikin Gida da na Kasashen Waje, a lokacin da take bayyana musu dalilai da kuma hujjar wajibcin ciwo bashin a Majalisa.

Ta ce shirin ciwo wannan bashi na cikin Shirin Raya Kasa na Zangon 2016 zuwa 2018 da Gwamnatin Tarayya ta shirya tun a wancan lokutan.

Zainab ta ce idan Majalisa ta amince, to za a ciwo basussukan ne har aji bakwai daga wasu bankuna da cibiyoyin hada-hadar kudade na waje.

Minista ta yi karin hasken cewa za a ciwo wannan bashi har a madadin jihohin kasar nan, kuma Tarayya ce za ta rika dibar kason kudaden jihohi ta na biya musu bashin a nan gaba.

Ba ta dai bayyana sai nan da shekara nawa za a fara biyan bashin ba. Sannan ba ta yi bayanin ko nawa tarayya da jihohi za su rika biya a duk wata har a gama biyan bashin idan an ciwo ba.

Daga cikin ayyukan da za a yi da kudaden, Minista ta ce za a gina titi nan mota, na jiragen kasa, ayyukan noma da inganta wutar lantarki da sauran su.

Ta kara da cewa za a yi amfani da wadannan kudade a bai wa masu Kananan Masana’antu (SME) lamunin inganta masana’antu, domin samar da ayyukan yi ga dimbin jama’a.

Zainab ta ce tulin bashin da Najeriya ta ciwo ba wata matsala ba. Matsalar da kawai aka fuskanta, wadda ita ce ta fi damun gwamnati, ita ce matsalar rashin isassun kudaden shiga aljihun gwamnati.

PREMIUM TIMES HAUSA ta buga wani labari a cikin makonni biyu da suka gabata, inda Babban Bankin Najeriya (CBN) ya nuna damuwa kan yawan basussukan da Najeriya ke ciwowa.

Baya ga Ministar Harkokin Kudade, Ministan Ayyuka Raji Fashola da na Yada Labarai, Lai Mohammed da Katamar Ministar Sufuri, Gbemisola Saraki, sun je a gaban kwamitin majalisa a ranar sun kare dalilan da za su ciwo bashi a ma’aikatun su.

Haka jami’an gwamnatin jihar Kogi, Katsina da Kaduna, su ma sun je domin gabatar da dalilan da za su ciwo basussuka, tare da bayanin abin da za a yi da bashin idan aka ciwo.

Shugaban Kwamitin Lura da Basussuka, Clifford Ordia, ya yi kira ga sauran ma’aukatu da Hukumomin da ba su je sun yi bayanin abin da za su yi da bashin da za su ciwo ba, su gaggauta zuwa su yi bayani.

Share.

game da Author