Manoma a jihar Kano sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta kara ware kudade domin inganta fannin aiyukan noma a kasar nan.
Manoman na farin ciki da shirin talllafawa manoma na gwamnatin tarayya wato ‘Anchors Borrowers Programme (ABP)’ saboda yadda shirin ke taimaka wa manoma.
Shugaban kungiyar manoman Najeriya (AFAN) Farouk Rabiu da manoman jihar Kano suka nuna haka a hira da suka yi da PREMIUM TIMES a garin Kano.
Rabiu ya ce tun a shekarar 2015 gwamnatin Buhari ta kirkiro da wannan shiri na ABP domin tallafawa manoma da basussuka da kayan aikin noma.
Ya kuma ce shirin ABP ya taimaka wajen karfafa gwiwowin manoma inda a yau amfanin noman da ake samu a kasar nan ya karu matuka sannan mutane da dama sun samu aikin yi.
Rabiu ya yi kira ga gwamnati da ta ci gaba da wannan shiri na APB, kada ta saurari masu kira da a dakatar da shirin don kin biyan basussukan da wasu manoma suka ki yi.
Ya ce manoma sun biya basukan da suka karba da a dalilin haka an asamu karin yawan shinkafar da ake nomawa a fadin kasar nan da kusan kashi 95%.
Rabiu ya yi kira ga gwamnati da ta inganta noman alkama a kasar nan a maimakon kashe Naira tiriyan daya da take yi wajen shigo da alkama daga kasar Rasha.
Ya ce akalla da Naira biliyan 20 gwamnati za ta iya noma gonan alkama hekta 100,000 wanda zai isa ciyar da kasar nan.
Wani manomi, Sa’adu Ali yace rashin tallafa wa manoma da kayan aikin da wuri ya sa shi asaran dukiyarsa masu yawa a shekarun baya da suka gabata.
Ali ya yi kira ga gwamnati da su rika tallafawa manoma da kayan aiki a lokacin da ya kamata cewa yin haka zai sa a samun amfanin gona mai yawan gaske a kasar.
Discussion about this post