A gaba na aka bindige wadanda suka shirya wa Janar Murtala Juyin mulki – Farida Waziri

0

Karshen makon da ya gabata kafafen yada labarai sun cika da bayanan tsakure daga littafin Farida Wazari, mai suna Farida Waziri: One Step Ahead.

Ita ce tsohuwar Shugabar Hukumar EFCC, wadda ta gaji shugaban farko, Nuhu Ribadu.

PREMIUM TIMES HAUSA ta tsakuro wa masu karatu yadda aka shirya wa tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo da Janar Shehu ‘Yar’Adua mai ritaya, shari da gadar-zare, aka ce su na da hannu a yunkurin juyin mulkin 1995, wanda Farida ta ce duk karya ce kawai da sharri.

Farida wadda a lokacin ta kasance cikin lauyoyin gabatar da kara a kwamitin binciken wadanda ake zargi.

A yau kuma mun dauko maku wani tsakuren, inda Farida ta bayar da labarin yadda aka bindige wadanda aka kama da laifin yi wa tsohon shugaban kasa Janar Murtala a gaban ta, abin da ta ce yanayin kisan ya dade ya na tayar mata da hankali matuka.

Mau karatu ga ku, kuma ga bayanan da Farida ta yi a cikin littafin na ta.

Lokacin da aka shirya wa Janar Murtala juyin mulki a karkashin Laftanar Kanar Bukar Dimka, a ranar 13 Ga Fabrairu, Farida ta na mukamin ASP ta dan sanda. Sun yi nasarar kashe Murtala da wasu da dama.

Ita kuwa Hassana matar Dimka wanda ya kashe Murtala, kuma jagoran masu yunkurin juyin mulki, kawar Farida ce sosai. Kuma a bangaren masu binciken manyan laifuka inda Farida ke aiki a lokacin ne aka yi binciken wadanda ake zargi da aika mummunan kisan gillar.

“Hassana Burundua matar Dimka kawa ta ce sosai, kuma tsohuwar ‘yar sanda ce abokiyar aiki na, amma ta yi ritaya ko a lokacin da aka yi yunkurin juyin mulkin.

“Hankali ta ya dugunzuma kwarai jin muryar mijin ta Dimka ya na sanarwar juyin mulki, saboda na san hatsarin da ke tattare da wanda ya yi yunkurin juyin mulki.

Farida ta ga wasu da dama wadanda aka kama a kan yunkurin juyin mulki, saboda a shashen bincike na musamman inda ta yi aki ne aka tsare su.

Sannan kuma wani tarihin da da ta rubuta a littafin ta shi ne, yadda aka kashe wadanda aka yanke wa hukuncin kisa a kan juyin mulkin a gaban idon ta.

“Ina kallo aka bindige su gefen ruwan teku a Bar Beach, Lagos. Lokacin da na ga yadda aka ragargaza jikin su da harsasai, ga naman jikin nan ja wur cikin jini, hankali na ya yi matukar tashin da kawai sai na tsere na nufi gida a gigice. Na shige daki na kawanta, na rasa abin da ke min dadi.

“Sai da na shafe watanni ko ganin danyen nama ban a son yi, ballanta idan an dafa na dandana.

“Amma shi Dimka ba a ranar aka kashe shi ba, domin da ya ga ba su yi nasara ba, sai ya boye, kuma ba a samu nasarar kama shi ba, sai bayan makonni uku da yin aika-aikar da suka yi.

Yadda Sojoji Suka Ritsa Matar Dimka a Gida – Farida

“Matar Dimka, wato Hassana ta shaida min cewa ta tashi da safe kawai sai ta ga sojoji na shigowa gidan ta, ta bayan gidan, su na dira ta cikin lambun gidan.

Suka ce mata sun je ne domin su jira Oga, wato mijin ta.

“Jin haka sai ta tambaye su ta ce me ke faruwa ne? Suk ace mata ba ta sani ba? To ta je ta saurari radiyo.

“Hassana ta gigita matuka jin muryar mijin ta ya na sanarwar yayi juyin mulki, saboda ta san hatsarin da ke tattare da wanda duk ya shiga cikin juyi ko yunkurin juyin mulki.

Dimka dai ya yi nasarar komawa gida, ya hanzarta ya gudu bayan ya dauki wasu ‘yan kayayyakin sa.

“Ba a kama shi ba sai bayan makonni uku da yunkurin juyin mulkin wanda bai yi nasara ba, sai dai janyo asarar shugaban kasa Murtala da aka yi.”

“Can sai ta rika jin tafiyar sojoji da tankar yaki zuwa gidan su. Ta ji wani soja na magana a lasifika, ya na cewa, ‘kada wanda ya yi harbi, har sai na ce a yi harbi tukunna.

“Daga nan sai Hassana ta shige cikin daki. Katsam sai ji ta yi amsa kuwwa na amsawa da babbar murya, ana gargadi: “Duk wanda ya san ya na cikin gidan nan, to ya dora hannun sa a kai, ya fito.”

“Da dora hannayen ta a kai, ta fito. Nan take aka daura mata ankwa a hannu.”

Share.

game da Author