2023: Kyan shi dai Idan Buhari ya sauka, dan kudu ya dare – El-Rufai

0

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya ce shugaban cin Najeriya a 2023, sai yankin Kudu.

Ya ce yin haka ne kadai zai kara karfin dankon zumunci a tsakanin ‘Yan kudu da Arewa sannan ya daidaita siyasar kasar nan.

Tun kafin El-Rufai ya fadi haka ranar litinin, tsohon shugaban kasa Ibrahim Babangida ya fadi irin haka a hira da yayi da talavijin din Channels.

Sai dai shi IBB ya nuna idan ma zata koma yankin kudun, Inyamirai ne yafi dace wa su yi. Shi ko El-Rufai bai ayyana ko wace kabila bace a kudun za ta karba.

Tun da dadewa ‘yan siyasan Najeriya suka shirya salon mulki na karba-karba a tsakanin kudu da Arewa. Wannan tsari dai ba a dokar kasa ta ke ba.

” Duk dai ba a rubuce take ba, duk kasa aan yarda da wannan tsari na karba-karba a tsakanin kudu da arewa.

” A jam’iyya irin PDP, su har rubuta tsarin karba-karba suka yi amma suka wancakalar da wannan tsari a 2015. A ganina ya kamata duk wani dan siyasa da ya san ciwon kansa sannan yake mutanta siyasa ya amince da wannan tsari. Sai dai kuma ida abubuwa sun cukuikuye dole sai dai canja hakan, wannan abu ko menene shi?

” Shugaba Yar’Adua ya rasu a kan mulki. Hakan ya sa dole Jonathan ya karisa mulkin. A shekarar 2011, da yawa yan siyasan Najeriya sun yi ta kira ga Jonathan da ya sauka, wani dan Arewa ya zo ya cika sauran shekara hudun ‘Yar Adua. Ni ina daga cikin wadanda suka hana haka. Domin rabo ya kai Jonathan ga zama shugaban Kasa.

El-Rufai ya ce da sanin jam’iyyar APC ta ki ta saka mulkin Karba-Karba, wato wannan yanki yayi sannan wani yankin ya yi mulki. Sai dai idan Buhari ya kammala mulkin sa dole za a zauna, ‘yan APC na Arewa a zabi mutum daya daga kudu. Hakan dai shine yafi dacewa a yi idan lokaci yayi.

Sai dai kima wasu da dama daga yankin Arewa suna ganin hakan ba shine daidai ba. Sun ce kujarar ta mai rabo ne, wanda ya fi jama’a kuma ya iya allon sa, ba kawai ace wai sai don wasu sun yi dole wasu su yi ba.

Share.

game da Author