Zulum zai gina gadar da babu irin ta a Arewacin Najeria a Maiduguri

0

Gwamnatin jihar Barno ta bada kwangilar gida babban gadar da babu irin ta a yankin Arewacin Najeriya.

Jihar Kano ce jihar da ta gina irin wadannan manyan gadoji a babban birnin jihar sai kuma Kaduna da take da irin wannan gada kwaya daya tal da yake a mahadar titin kawo da Mando.

Kwamishinan Ayyuka na jihar Barno ya bayyana cewa tuni har an baiwa kamfanin kasar Chana, EEC kwangilar aikin.

Yace gwamnati zata kashe naira biliyan 4.2.

A lokaci da yake kaddamar da fara aikin gina gadar, Gwamna Babagana Zulum ya ce tuni har sun mika wa Kamfanin EEC naira Biliyan 1.3 na fara aiki.

Ya kara da cewa ana sa ran za a kammala aikin nan da watanni 18 masu zuwa sannan ya kara da cewa babu wani abu da zai sa su dakatar da ayyukan da suka saka a gaba domin ci gaban jihar.

Yace gwamnati za ta gudanar da ayyukan ci gaba a fadin jihar kamar yadda ta yi alkawari duk da matsalolib hare-haren Boko Haram da take fama da shi.

Share.

game da Author