Gwamnan jihar Ebonyi David Umahi ya bada umurnin rufe wani asibiti mai suna St Vincent a dalilin rasuwar wani da aka kwantar bayan ya kamu da zazzabin lassa a wannan asibiti.
Bayanai sun nuna cewa an kwantar da Ephraim Ogaranya tare da wani danuwansa Uchechi a wannan asibiti ne a dalilin kamuwa da zazzabin lassa da suka yi.
Bayan wasu ‘yan kwanaki sai Ephraim ya rasu. Ganin haka kuwa sai likitocin asibitin suka aika da Uchechi asibitin kula da masu fama da cutar dake Abakaliki.
Da gwamna Umahi ya samu labarin haka sai ya bada umurnin a rufe asibitin St. Vincent sannan ya kuma umurci duk ma’aikatan asibitin tare da ‘yan uwansu na kusa su gaggauta yin gwajin zazzabin lassa a asibitin Abakaliki domin kada cutar ta yadu.
Gwamnan ya kuma umurci gidajen jaridun dake jihar da su wayar da kan mutane kan hanyoyin guje wa kamuwa da cutar.
ZAZZABIN LASSA
Zazzabin lassa cuta ce da ake kamuwa da ita a dalilin cudanyar bera da abincin da muke ci, sannu a hankali cutar tana ta afkawa mutanen kasar nan.
Ma’aikatan kiwon lafiya sun bayyana cewa za a iya kamuwa da cutar idan aka yawaita zama tare da wanda ya kamu da cutar sannan idan ba a gaggauta neman magani ba cutar na iya yin ajalin mutum.
A shekaran 2018 rahotanni sun nuna cewa an gwada jinin mutane 3,498 daga jihohi 23 da ake zargin sun kamu da cutar inda sakamakon gwajin ya nuna cewa mutane 633 na dauke da cutar sannan kashi 27 daga cikin su sun rasu.
Jihohin Edo,Ondo da Ebonyi na daga cikin jihohin da suke fi fama da wannan cuta a kasar nan a bisa rahotannin da suke baya ni akai.
Wadannan hanyoyi kuwa sun hada da;
1. Da zarar mutum ya kamu da zazzabi a tuntubi likita domin tabbatar da cutar da mutum ke dauke da shi.
2. Duk ma’aikacin kiwon lafiya da zai duba mara lafiya a asibiti ya tabbata yana sanye da safar hannu sannnan ya kuma tabbata ya wanke hannayen sa da kyau bayan ya gama duba mara lafiya.
3. Ma’aikatan kiwon lafiya su tabbatar sun nemi magani da zarar alluran da suka yi amfani da shi a jikin wanda ke dauke da cutar ya soke su.
4. A tabbata an tsaftace muhalli da kuma adana kayan abinci nesa da fitsari da kuma kashin beraye.
5. Ba a iya kamuwa da cutar zazzabin Lassa idan an taba wanda ke dauke da cutar amma za a iya kamuwa da shi idan yawu, jini ko kuma zufan wanda ke dauke da cutar ya taba wanda ba ya da shi