Ganin yadda ake kara yawan samun rashin tsaro da garkuwa da mutane a Girei, cikin Karamar Hukumar Girei, al’ummar garin sun fito sun yi zanga-zanga jiya Talata, tare da kiran Shugaba Muhammadu Buhari ya kai musu dauki.
Masu garkuwar, wadanda suka datse babbar hanyar shiga Yola, babban birnin Jihar Adamawa, sun rika daga kwalaye masu dauke da kakkausan rubutun da ke nuna rashin jin dadin abin da ke faruwa a yankunan su.
Wani shugaban matasan yankin mai suna Saidu Hamman Girei, ya bayyana dalilin zanga-zangar da su ke yi.
“A kullum babu fashi sai an dauki mutanen mu an yi garkuwa da su; wasu mazauna yankunan mu sun tsere gudun hijira daga gidajen su, saboda tsoron kada a zo a sace su a yi garkuwa da su. Ka gan mu nan a kullum ba mu iya barcin kirki, saboda tsoron masu garkuwa da mutane.
“Kwanan nan masu garkuwa da mutane sun shigo Girei sun kashe mutane. Sun kuma karbi kudade a Girei sun kai naira milyan 70.
Saidu ya kara da cewa matasan garin sun yi taro da sarakunan gargajiya domin yin sintirin awa 24 babu kakkautawa domin magance mabarnatan da ke garkuwa da mutane.
“Wannan yunkuri da muka yi ya haifar da samun ci gaba, domin mun samu nasarar damke wasu da ake zargi, mun kuma samu makamai na binidigogi, albarusai da sauran hujjoji masu tabbatar da cewa su na garkuwa da mutane.” Inji Saidu.
“Daga cikin wadanda aka damke, akwai wani da ya shaida mana cewa shi mai garkuwa da mutane ne, kuma ya lissafa wasu abokan tafka garkuwa da mutanen da suke yi har mutane 9. Muka dauke shi ya kai mun inda suke boye.
“Amma abin mamaki shi ne, ‘yan mintina kadan bayan mun damka wadannan masu garkuwa da mutane ga ‘yan sanda, sai umarni wai ya zo ‘daga sama cewa a gaggauta sakin su.” Cewar Saidu.
Wani mai zanga-zanga da ya ce sunan sa Mallum Girei, ya zargi ‘yan sanda da hadin baki da masu garkuwa da mutane.
Ya ce, “mutane sun gaji da wannan fuska-biyu da jami’an tsaro ke nunawa. Ba wannan ne karo na farko da aka taba kama masu garkuwa da mutane amma ‘yan sanda suka sake su ba.”
Sai dai kuma Kakakin Yan Sanda na Jihar Adamawa, Sulaiman Ngoruje, yace jami’an tsaro na nan na bincike, ya kuma karyata cewa ana hada baki da su ana aikata garkuwa da mutane ko ana sakin masu garkuwa damutane.