ZABEN KANO: Abdulmumini Jibrin ya yi sallama da majalisa, Doguwa ya dawo

0

A zaben da aka gudanar ranar Asabar a Jihar Kano, fitaccen dan siyasa kuma dan majalisar dake wakiltar Kiru/Bebeji a majalisar Tarayya, Abdulmumini Jibrin, ya sha kayi.

Farfesa Abdullahi Arabic, da ya bayyana sakamakon zaben ya shaida cewa Ali Datti-Yako na jam’iyyar PDP ne ya lashe zaben kujerar.

Abdulmumini ya yi takara a jam’iyyar APC.

Datti na PDP ya samu kuri’u 48,601, shi kuma Jibrin na APC ya samu kuri’u 13,587.

Shi kuma Ado Doguwa wanda shine shugaban masu rinjaye na majalisar Tarayya, yayi nasarar dawo inda yayi wa abokin takarar sa na jam’iyyar PDP kifa daya kwala.

Doguwa ya doke Salisu Yasha’u na jam’iyyar PDP da kuri’u 66,667.

Salisu ya samu kuri’u 6,322.

Share.

game da Author