ZABEN AKWA IBOM: Akpabio ya sha kayi

0

Duk da karfin Iko da ya ke da shi na ministan yankin Neja-Delta, Sanata Akpabio Godswill ya sha kayi a zaben ranar Asabar.

A zaben kujerar sanata ta Akwa Ibom ta Arewa Maso Yamma, Chris Ekpenyong, ya samu kuri’u 134,717, inda ya kada tsohon sanata, Godswill Akpabio, da ya tashi da kuri’u 83,820.

Duk da cewa an bada rahoton tashin hankali a wurare da yawa musamman inda aka yi zabukan hakan bai sa PDP bata lallasa Akpabio ba na APC.

PDP ce ta lashe zabukan da aka sake a jihar kaf, duk da cewa ‘yan takarar APC biyu sun janye gab da za a fara jefa kuri’a.

Daya daga cikin su ya koka cewa tun farko bai yarda da malamin zaben da zai gudanar da zaben ba , sannan na biyu kuma ya ce kutun daukaka kara bata umarci hukumar zabe ta sake zabe a yankin sa ba.

Share.

game da Author