Kotun koli ta dage yanke hukuncin zaben gwamnan jihar Sokoto zuwa ranar 20 ga watan Janairu, rana daya da na gwamnan Kano.
Idan ba a manta ba Cif Jojin Najeriya, Babban Mai Shari’a Tanko Muhammad ya bayyana cewa za a yanke shari’ar zaben gwamnan Kano a ranar 20 Ga Janairu, 2020.
Hakan ya biyo bayan dogon lokacin da lauyoyin mai kara Abba Yusuf da na wanda ake kara, Abdullahi Ganduje da INEC suka dauka ana tabka mahawara a gaban alkalan Kotun Koli su bakwai.
Alkalai 7 ne dai ke zaman sauraren kararrakin gwamnonin da ake sa ran yanke hukunci daga yau Talata.
Babban Mai Shari’a Mohammed Tanko, kuma Cif Joji na Najeriya, shi ke shugabantar alkalai 6, sais hi cikon na 7 din.
Tambuwal ya lashe zaben Sokoto da kuri’u dari uku ne da ‘yan kai kacal wanda jam’iyyar APC ta kalubalanci wannan sakamako a kotu.
Kano: Tsakanin Abba Gida-gida da Ganduje
Tun da farkon kafsawa dai lauyan Abba Yusuf Adegboyega Awomolo ya bayyana a rubuce cewa ya na so kotu ta bada umarnin a ci gaba da sauraren yanke hukuncin wannan kara.
Kuma ya na rokon kotu ta dubi rashin adalcin da aka yi wa wanda ya ke karewa, wato Abba na jam’iyyar PDP, sannan ta kwato masa hakkin sa daga hannun Gwamna Abdullahi Ganduje da kuma jam’iyyar APC.
Awomolo ya yi tsokacin cewa mai bayyana sakamakon zabe da shugaban tattatara sakamakon zabe ya soke zaben rumfuna 207, ya ce wai zabe bai kammalu a wuraren ba, daga nan ya sa wata ranar 23 Ga Maris, 2019, aka sake zabe.
Daga nan ya ce soke zaben da aka yi bayan da aka rigaya aka bayyana sakamakon zabe, rinto ne, giriftu ne, kuma shugaban zaben ba shi da ikon yin haka a dokar kasa.
Wannan babban lauyan na Abba Yusuf ya ce, “sakamakon zaben 23 Ga Maris, wanda aka ce shi ne zaben ‘inconclusive’ na rumfuna 207, haramtacce ne.”