Hukumar inshorar kiwon lafiya ta kasa (NHIS) ta sanar cewa nan ba da dadewa ba hukumar za ta fara aiki da tsarin inshoran kiwon lafiya na bai daya wato ‘Health Insurance scheme under one roof’.
An kafa hukumar NHIS ne domin tallafa wa mutane wajen biyan kudin asibiti. Sai dai hakan da aka yi ba a kai ga samun nasara ba har yanzu domin mafi yawan mutane basu cikin tsarin kuma kadan dake cikin shirin suna matukar kokawa da rashin samun biyan bukata.
A dalilin haka ya sa NHIS ta kawo tsarin bude inshoran kiwon lafiya a jihohi sannan ta kirkiro shiri na bai daya domin kula da aiyukkan da hukumomin inshorar ta tarayya da na jihohi ke yi a kasar nan.
Jihohin Legas, Delta, Anambra, Niger na daga cikin jihohi 20 din da suka kafa na su inshoran kiwon lafiya a jihohin su a kasar nan.
Shugaban hukumar NHIS Mohammed Sambo ya sanar da haka a wata zama da hukumar ta yi da hukumomin na jihohi.
Sambo ya ce bisa ga tsarin inshorar kiwon lafiya na bai daya inshorar kiwon lafiya ta tarayya za ta kula da ma’aikatan dake aiki da gwamnatin tarayya sannan hukumar za ta rika kula da ma’aikatan dake aiki a asibitocin ta da na jihohi.
Ya ce hukumar ta tsara hanyoyi domin bayyana wa kowacce bangare tsarin aiyukkan da ya kamata a yi domin cin ma burin samar wa mutane kiwon lafiya mai nagarta sannan a farashi mai sauki.
Ya ce nan ba da dadewa ba hukumar NHIS za ta shirya taron sanin makaman aiki da ma’aikatan hukumomin na jihohi.