Yawan mutanen dake amfani da dabarun bada tazarar iyali ya karu a jihar Kano

0

Dakta Habbi Sadauki dake aiki da Kungiyar Dprc ya bayyana cewa an samu karuwa matuka kan yawan mutanen dake amfani da dabarun bada tazarar iyali a jihar Kano.

Sadauki ya fadi haka ne a taro da aka yi domin sanin karbuwar dabarun bada tazarar Iyali da kungiyar Dprc ta shirya a garin Kano.

Ya ce lallai an samu ci gaba a yawan mutanen dake amfani da dabarun bada tazarar iyali domin a shekaran 2013 adadin yawan mutanen dake amfani da dabarun sun kai 1.3 amma a shekarar 2018 ya karu zuwa 5.8.

Bincike ya nuna cewa idan har gwamnati bata yi komai ba wajen wayar da kan mutane game da sanin alfanun yin amfani da dabarun bada tazarar iyali nan da shekarar 2050 masu zuwa adadin yawan mutane a jihar zai zarce miliyan 50.

A dalilin haka gwamnan jihar Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta raba wa mutane dabarun tazarar iyali kyauta da kuma shirya tarukka domin wayar da kan mutane mahimmancin yin amfani da dabarun.

Bayan haka shugaban hukumar NIPSS Habu Gumel ya bayyana cewa hukumar za ta hada hannu da Dprc domin inganta yin allurar rigakafi, inganta aiyukan cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko da wayar da kan mutane kan muhimmancin amfani da dabarun tazarar iyali.

Gumel ya ce dole a samar da hanyoyi da za a bi don rage yawan mutane a kasar nan ya zama dole domin bincike ya nuna cewa nan da shekaru 50 masu zuwa adadin yawan mutane a kasar nan zai kai miliyan 289.

Share.

game da Author