‘Yan sanda sun kashe ‘yan bindiga biyu, sun ceto mutane 20 a Kaduna

0

Rundunar ‘Yan sandan jihar Kaduna ta bayyana cewa ta ceto mutane Takwas da aka yi garkuwa da su a Mararaban Jos titin Kaduna zuwa Zariya sannan dakarun ta sun kashe biyu daga cikin masu garkuwan.

Rundunar ta kuma ce ta ceto wasu ma’aikatan kamfanin ‘Airtel’ guda uku da mutane Tara da aka yi garkuwa da su ranar 14 ga watan Janairu.

Kakakin rundunar Yakubu Sabo ya sanar da haka ranar Laraba inda ya kara da cewa mutane Takwas din da aka yi garkuwa da su matafiya ne daga jihar Kano zasu Abuja a mota kirar Sharon.

“ Mun yi batakashi da maharan daga nan muka ci karfin su har muka kashe mutane biyu cikin su kuma muka ceto wasu.

” Daga cikin mutanen da muka ceto akwai Aisha Umar, Samira Ibrahim Dakata, Safiya Idris, Hauwa Aliyu, Aisha Yakubu, Ma’aru Adam, Safiya Audu da Yahaya Bello duk daga jihar Kano.

Baya ga haka Sabo yace rundunar ta ceto ma’aikatan kamfanin ‘Airtel’ guda uku masu suna Henry Agim, Kamal Raman da Segun Adejimoh.

Ya ce rundunar ta gano maboyar wadannan masu garkuwa da mutane a kauyen Maidaro dake karamar hukumar Giwa.

Sabo ya ce rundunar ta gamu da wasu mutane Tara da aka yi garkuwa da su tare da sarkin Potiskum ranar 14 ga watan Janairu.

“ Daga cikin su akwai Abdulhafiz Wakil, Abdul Wasiu Jimmoh, Mujittaba, Hajara Usman, Emmanuela Dimka, Dahiru Isa da wasu mutane uku.

A karsh kwamishinan ‘yan sanda Umar Muri ya yabawa hadin kan da mazaunan kauyukan suke ba ‘yan sanda.

Share.

game da Author