‘Yan sanda sun damke matar da ta bankada kishiya da dan ta rijiya a Kano

0

Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kano, ta bayyana damke wata mata mai shekaru 30, mai suna Hauwa Lawal wadda ake zargi da banka kishiyar ta cikin rijiya.

Ana zargin Hauwa da bankada kishiyar ta mai suna Zuwaira Sani, mai shekaru 35 rijiya, tare da dan Zuwairar mai watanni 18 da haihuwa.

Kakakin Rungunar ‘Yan Sandan Kano, Abdullahi Haruna, ya tabbatar da kama matar a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai, jiya Lahadi a Kano.

Haruna ya ce jami’an su sun samu rahoto a ranar Juma’a cewa Hauwa ta banka kishiyar ta mai suna Zuwaira da dan ta cikin rijiya, a kauyen Rurum, cikin Karamar Hukumar Rano.

“Wadda ake zargi da aikata laifin ta samu sabani da kishiyar ta ta, daga nan suka kaure da rikici, inda Hauwa ta tunkuda Zuwaira cikin rijiya, tare da jinjirin ta mai watanni 18, mai suna Mustafa Gambo.”

An tunkuda Zuwaira da dan ta da ke goye a bayan ta, cikin rijiyar wadda ke cikin gidan su.

Haruna ya ce Kwamishinan ’Yan Sanda na Kano, Habu Amadu ne da kan sa ya bada umarni a kamo Hauwa cikin sa’o’i 24 bayan da aka ji labarin cewa ta gudu bayan ta banka kishiyar ta da dan kishiyar cikin rijiya.

“Jami’an Operation Puff Adder sun shiga farautar ta, har suka kamo ta wajen 1: 17 na dare.

“An gaggauta tsamo wadanda aka tura rijiyar, tare da gaggauta kai su Asibitin Rano, inda a can likitoci suka tabbatar da cewa Zuwaira ta rasu, amma dan ta bai mutu ba, kuma an sallame shi daga asibitin.

“Wadda ake zargin ta amsa laifin ta a gaban ’yan sanda.”

A yanzu an maida wannan bincike a bangaren CID masu binciken manyan laifuka na jihar Kano.

Haruna ya ce da zaran an kammala bincike, za a tura Hauwa a gaban alkali domin a yi mata shari’a.

Share.

game da Author