‘Yan sanda sun damke dillalin bindigogi biyu, sun kyale Amosun dillalin dindigogi 1,000

0

A wani abu mai kama da an bugi taiki an kyale jaki, watanni shida kenan amma har yau jami’an tsaro na ’yan sanda da sauran fannoni sun ki kama Sanata Ibikunle Amosun, wanda aka fallasa ya shigo ya yi sumogal din bindiga samfurin AK-47 guda 1,000.

Sai dai kuma duk da kiraye-kirayen da ‘yan Najeriya suka rika yi cewa kamata ya yi a kama shi tunda ya saura daga mukamin gwamna, ba shi da rigar kariya, an yi biris.

Amma kuma yayin da aka zargi wani dan kasuwa mazunin Lagos da laifin safarar bindiga samfurin fistol biyu, sai ‘yan sanda suka tashi tsaye farautar sa, kai ka ce farautar shugaban ‘yan ta’addar duniya suke yi.

Ranar Larabar da ta gabata, sai ga Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Lagos Hakeem Odumosu ya na bayanin abin da ya kira gagarimar nasarar damke Samuel Uche a yayin da ya ke kokarin saida bindigogi kirar fistol guda biyu.

Kwamishinan ’Yan Sanda ya gabatar da Uche a gaban manema labarai, inda ya bayyana musu cewa “Uche ne babban gogarman safarar makamai da ake nema ruwa a jallo.”

Ya ce an kama Uche a lokacin da ya ke kokarin sayar da bindigogi biyu a kan kudi naira 250,000 a Oshodi, ranar 3 Ga Janairu.

An ruwaito cewa ya amince da aikata laifin da aka zarge shi da aikatawa.

Yayin da aikin jami’an ‘yan sanda wajen dakile manya da kananan laifuka ya shafi kowa duk girma da mukamin mutum, amma alamu da hujjoji na nuna cewa akwai wadanda ake kauda kai daga

Ba Uche ne farkon kamawa da laifin safarar makamai ana kullewa a kurkuku ba. An sha kama da dama kafin shi, kuma ana daure su shekaru masu tsawo ko yawa a gidajen kurkuku.

Cikin watan Mayu, 2019, Babbar Kotun Jihar Oyo ta daure wani mutumm shekaru 120 saboda samun sa da laifin safarar makamai.

Amma kuma cikin watan Yuni, 2019, PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda Ibekunle Amosun ya yi sunkurun sumogal din manyan bindigogi da albarusai dubbai, a lokacin da ya na gwamna, ba tare da samun umarni daga gwamnatin tarayya ko jami’an tsaro ko dokar Najeriya ba.

An tabbatar da cewa Amosun wanda ya kammala wa’adin san a gwamna, a yanzu haka makusancin Shugaba Muhammadu Buhari ne.

Ya shigo da AK-47 1,000, harsasai milyan biyu da sauran kayan makamai daban-daban.

Yayin da har yanzu hukumomin tsaron kasar nan ba su kama Amosun ba, shi kuma ya ci gaba da harkokin sa a matsayin sa na daya daga cikin Majalisar Dattawa na Najeriya.

Amosun su ne manyan dattawan Najeriya, kuma su ne masu yi wa ‘yan Najeriya dokar da za su bi.

Share.

game da Author