Gwamnatin jihar Kano ta rufe wani gidan marayu mai suna ‘Du Merci Orphanage Home’ dake Nomansland bayan ta ceto yara marayu 19 daga gidan.
Gwamnati ta ta yi haka ne bayan ta gano cewa an kafa wannan gidan marayu ba bisa doka ba.
Mai bai wa gwamnan jihar shawara kan jin dadi da walwalar yara kanana da mata Fatima Dala ta sanar da haka inda ta kara da cewa gwamnati ta aika da wadannan yara 19 zuwa gidan marayun dake mallakin gwamnati wato ‘Nasarawa Orphanage Home’.
Fatima ta ce bincike ya nuna cewa wani Solomon Richard ne ya bude wannan gida amma ba a matsayin gidan marayu ba, an bude shi ne a matsayin ofishin wata kungiya mai zaman kanta.
Tace tun da ya bude wannan gida, shekaru 25 kenan Solomon na tara yara kanana da sunan yana tallafa musu.
Fatima ta ce an tuni jami’an tsaro suka cafke shi sannan nan ba da dadewa ba za agurfanar da shi a kotu.
” Wannan abu da muka yi ba shi da alaka da wani kabila ko addini. Mun yi haka ne domin mu ceto wadannan yara da ka killace da sunan wai ana tallafa musu , marayu ne.
Fatima ta yabawa goyan bayan da jami’an tsaro suka bada wajen kubutar da wadannan yara sannan ta yi kira ga mutane da su rika sanara da hukumar ire-iren wadannan gidaje da ba a san dasu ba.
Idan ba a manta ba a watan Nuwanbar 2019 rundunar ‘yan sandar jihar Kano ta kama mutane Takwas da suke da hannu a yin garkuwa da yara Goma daga jihar.
Binciken ‘yan sanda ya nuna cewa an sato wadannan yara ne daga yankunan daban daban na jihar domin siyar da su a jihar Anambra.
Discussion about this post