A ranar Alhamis ne daya daga cikin ya’yan shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Hannan Buhari ta dare jirgin shugaban kasa zuwa garin Bauchi domin yin ziyarar gani da ido.
Ganin wannan jirgi ya sauka a garin Bauchi mutane da dama sun yi zaton Shugaba Muhammadu Buhari ne ya kawo ziyarar bazata ashe, yarsa ce Hanan.
Uwargidan gwamnan jihar Bauchi ce ta tarbi Hanan a filin jirgin saman jihar.
Bayan tattaunawa da suka yi a gidan gwamnati da ke Bauchi tare da Uwargidan gwamna Bala Mohammed ta kai ziyara fadar sarkin Bauchi.
Anan ma an nuna mata adon dawakai da wasu kayayyakin tarihi na masarautar Bauchi.
Daga nan sai ta dare jirgin ta koma Abuja.
Tun bayan haka ‘yan Najeriya suka rika fitowa suna sukar wannan dama da shugaban Buhari ya ba ‘yar autar sa wato Hanan na yin amfani da jirgin fadar shugaban kasa da ya kamata shi ne zai rika hawa.
Kungiyar kwadago ta koka kan amfani da wannan jirgi da yar Buhari ta yi ta na mai cewa a wannan lokaci da gwamnati ke kukan babu kudi a kasa sai a dauki jirgin da yafi kowanne daraja a kasa a baiwa yarinya ta tafi yawan bude ido.
Manyan Lauyoyin kasar nan da suka hada da Femi Falana sun yi tir da wannan abu da fadar gwamnati ta yi.
Falana ya ce ba maganan doka ba kawai, abinda da dokar kasa ta shardanta shine shugaban Kasa da Mai dakin sa, sannan mataimakin sa da mai dakin sa, sai kuma shugabannin majalisar kasa da kuma babban jojin kasa ne kawai za su iya amfani da wannan jirgi.
Amma haka kawai don kina ‘yar shugaban kasa sai a dauki jirgin da shugaban kasa ke hawa a baki ki tafi yawan bude ido, babu shi a dokar kasa.
” Hakan fa kamar ta dauki motar sa ce ta shiga ta tafi yawon ta don tana ‘yar shugaban kasa. Duk da yana dauke da tambarin kasa.
Chidi Odinkalu da shima lauya ne kuma mai rajin kare hakkin dan Adam, yayi Allah wadai da wannan abu da aka bari ‘yar autar shugaba Buhari ta yi.
Odinkalu ya ce ana yi wa Buhari ikirarin shi mai gaskiya ne sannan mai sanin ya kamata bai kamata ace ya bari anyi haka ba, ” Ko da yake yanzu ya zama da bam.”
A martani kan wannan cece-kuce da ake ta yi da ta maida, fadar shugaban ka sa ta shaida cewa iyalan shugaba Buhari na da ikon dana jirgin shugaban kasa.
Garba Shehu ya bayyana cewa lallai Hanan na da ikon darewa jirgin shugaban kasa ba tare da tana tare da shi ba.
Ya ce sai da aka bi dukkan hanyoyin da ya kamata abi domin ta samu damar yin amfani da jirgin kafin ta garzaya garin Bauchi.
Discussion about this post