‘Yan Najeriya sun nuna rashin amincewa Shugaba Muhammadu Buhari ya kashe naira bilyan 37 wajen yi wa Majalisar Tarayya kwaskwarima ba.
A wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a da PREMIUM TIMES ta fitar, akasarin jama’a ba su goyi bayan a kashe wadannan makudan kudade a gyaran Majalisa ba.
Daga cikin mutane 2,216 wadanda suka kada kuri’a, 1,380 ba su amince ba. Mutane 124 kawai suka ce a kashe kudin wajen kwaskwarima, tunda Shugaban Kasa ya rigaya ya sa hannun amincewa.
Saura 712 kuma suka ce maganar gaskiya kudaden sun yi yawa sosai, don haka a zabtare su kafin a fitar a yi aikin.
Sun ce ai ko mahaukaci ya san kudin sun yi yawa.
Idan ba a manta ba, Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmed Lawan ne ya bayyana cewa Buhari ya amince a yi kwaskwarima ga Majalisa ta naira bilyan 37, wadda suka cusa a cikin kasafin 2020.
Ya ce Buhari ya amince ne bayan da shugabannin majalisar suka yi takakkiya, suka same shi suka nuna masa wajibcin haka.
Wannan batu dai, musamman jin zunzurutun adadin kudaden ya harzuka ‘yan Najeriya har da dama suka rika cewa wannan damfara ce da wala-wala kawai.
Tuni dai har wasu daidaikun mutane 500 sun garzaya Babbar Kotun Tarayya, sun nemi kotu ta hana Buhari da Ministar Harkokin Kudade, Zainab Ahmed fitar da kudaden.
Kada a manta, cikin 2013 lokacin mulkin Goodluck Jonathan, ya sa hannun amincewa a kashe naira bilyan 40.238 domin yi wa Majalisa kwaskwarima a cikin shekaru uku da wata hudu.
Said dai PREMIUM TIMES ta kasa gano shin an fitar da kudaden ko kuwa?
Kokarin jin yadda aka yi da kudin ya ci tura a Ma’aikatar Harkokin Kudade. Sannan an yi kokarin jin ta bakin kakakin Kamfanin Julius Berger, kamfanin da aka bai kwangilar, domin sanin ko an ba su kudin? Amma Akeem Taufeek bai daga wayar sa ba, kuma bai maido amsar sakon tes da aka yi masa ba.