Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Ondo ta tabbatar da labarin sace wani jigon jam’iyyar APC a ranar Lahadi da ta gabata.
’Yan bindiga sun yi masa takakkiya har gidan sa a unguwar Ibaka, da ke Akungo Akoko cikin Karamar Hukumar Akoko ta Kudu Maso Yamma, suka yi awon-gaba da shi.
An tabbatar da cewa bayan da maharan suka isa gidan, sai da suka yi kaca-kaca da gidan, sannan suka cusa shi cikin motar su, suka tsere da shi a cikin motar sa.
Ajulo dai shi ne shugaban bangaren APC mai jayayya da daya bangaren, na Mazaba ta 13, cikin Karamar Hukumar Akoko ta Kudu maso Yamma a Jihar Ondo.
Abokin sa mai suna Tolu Babalaye, wanda aka yi al’amarin a gaban sa, ya bayyana cewa wadanda suka arce da shi din dai kwanton-bauna suka yi masa kusa da gidan sa.
“Sai da suka yi kaca-kaca da gidan sa kafin su arce da shi a cikin motar sa.” Cewar Babalaye, wanda ya kara da cewa a cikin motar sa kirar Toyota Sienna suka bi motar da suka saka shi, domin su samu saukin arcewa salum-alum.
“Sai da suka rika dirka harbin bindiga barkatai domin su firgita jama’a, kowa ya gudu ko ya kwanta ya kasa fitowa.”
Ya ce har yanzu wadanda suka gudu da shi ba su kira wa yaba, balle a ji abin da suke so a biya su kafin su sake shi.
“Amma dai an kai rahoton yin garkuwar da shi a Dibijin na ’yan sandan Akoko din.”
Shi kuma Kakakin ‘Yan Sanda na Jihar Ondo, Femi Joseph, ya ce ana nan a na gudanar da bincike da kokarin ceto shi.
Garkuwa da mutane ya zama ruwan-dare a Jihar Ondo, kuma akasari ba a jin rahotannin abin da ke faruwa a kafafen yada labarai, wasu kuma ba a kai rahoto ga jami’an tsaro.