A yanzu haka Shugaban Karamar Hukumar Afijio da ke Jihar Oyo, Samuel Aderemi na can ya na jiyya a wani asibiti, bayan da wasu gungun ‘yan jagaliya suka yi masa dukan tsiya.
Al’amarin ya faru ranar Laraba, a lokacin da shugaban da ‘yan majalisar sa suka yi kokarin sake shiga Harabar Karamar Hukumar da ke garin Jobele.
Aderemi na cikin shugabannin da Gwamna Seye Makunde na Oyo ya tsige cikin 2019. Sun yi kokarin sake shiga hedikwatar ne, bayan an nada su ne a karkashin waccan gwamnatin APC ta jihar Oyo.
PREMIUM TIMES ta tabbatar da cewa ‘yan jagaliyar sun kewaye Aderemi suka yi dukan tsiya. Bayan da suka yi masa laga-laga, sun kuma cumuimuye shi suka jefa a mota, suka arce da shi.
Amma bayan sa’o’i biyu jami’an tsaro sun ceto shi. Har zuwa lokacin da ake rubuta wannan labari dai Aderemi na can kwance a wani kebantaccen asibitin da ba a bayyana inda ya ke ba.
Tsohon Shugaban Kungiyar Shugabannin Kananan Hukumomin Jihar Oyo, Ayodeji Abass-Aleshinloye ya tabbatar da afkuwar wannan mummunan lamari.
Discussion about this post