Yadda wani ya sace ruwan Inabi mai tsarki a coci ya kwankwade

0

Kotu ta a jihar Legas ta fara shari’ar da aka shigar a gabanta na wani mutum da ya dauke kwalaben ruwan inabi da ake amfani da shi a coci wajen aikin bauta.

Wannan ruwan Inabi da ake kira ‘Communion Wine’ akan rabawa mabiya ne su dan sha a lokacin da ake yi musu addu’a domin samun kari’a daga shaidanu muggan mutane.

Fasto ne kan rabawa mabiya a coci sannan a wasu lokuttan har da dan gurasa da za a hada da shi.

Mabiya addinin kirista, sun bayyana cewa wannan abu ya samu asali ne tun a lokacin annabi Isa wanda shine suke koyi da shi.

Lauyan da ya shigar da karar Edet Akadu ya bayyana cewa Ajibola ya waske da kwalaben wannan ruwa ne ranar 24 ga wata Satumba 2019.

Akadu ya kuma kara da cewa ba ruwan Inabin ba har da sabulai da buhunan gishiri da suka kai Naira 46,000 ya dauke daga cocin.

“Sannan don diban albarka mutanen cocin sun iske Ajibola yana kwankwadan wannan ruwan inabi.

Sai dai bayan sauraren karar shi mai laifi Ajibola ya musanta aikata laifi.

Alkalin kotun K.O. Ogundare ya bada belin Ajibola a kan Naira 20,000 tare da gabatar da shaidu biyu.

Za a ci gaba da shari’ar ranar 5 ga watan Fabrairu.

Share.

game da Author