Yadda muka fafata da mahara a dajin Birnin Gwari – Dakarun Sojin Saman Najeriya

0

Darektan yada labaran rundunar sojojin saman Najeriya Ibikunle Daramola ya bayyana cewa dakarun sonojin saman sun fada wa harin kwantan bauna da wasu mahara suka afka musu.

Daramola ya kara da cewa da sona daya ya rasa ransa, wasu da dama kuma sun jikka, amma suna asibitin sojoji ana duba su.

Sojojin rundunar sojojin sama na 271 dake aikin samar da tsaro a Birnin Gwari sun fada wa harin kwantar bauna da wasu mahara suka kai musu a garin Unguwan Yako dake Titin Kaduna-Birnin-Gwari.

Sojojin sun fafata da maharan inda suka ci karfin su bayan an gwabza yaki da barin wuta.

Sai dai kash duk da maharan sun sha kashi a hannun sojojin sun kashe soja daya.

Wanda aka kashe, Mukhtar Ibrahim, an yi jana’izan shi ranar Juma’a sannan sauran da aka ji wa rauni suna kwance a asibiti a na duba su.

Karamar Hukumar Birnin Gwari, ta dade tana fama da matsalolin hare-hare daga mahara da ke boye a dazukan.

A kullum sai kaje ko an far ma wani gari ko kuma an yi garkuwa da mutane a wannan titi.

Gwamnati ta yi matukar maida hankali wajen samar da tsaro a wannan titi inda jami’an tsaro ke kai komo a wannan titi domin samar da tsaro ga matafiya da mazauna kauyuka.

Share.

game da Author