Yadda mahara suka far wa makarantar kwana suka arce da yara hudu a Kaduna

0

Mahara sanye da kayan sojoji kuma dauke da manyan bindigogi sun afka makarantar koyon zama malamin darikar Katolika da ake kira ‘Good Shepard Major Seminary School’ dake unguwar Kakau a garin Kaduna inda suka yi garkuwa da yara hudu cikin sama da yara 260 dake makarantar.

Ita dai wannan makaranta ta maza ce zalla.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna Yakubu Sabo ya bayyana cewa maharan sun afka wa makarantar ne da misalin karfe 12 na daren jiya.

” Maharan sun rika harbi ta ko ina domin tsorata jama’a kafinnan suka afkawa wa makarantar kwanan.

Sabo ya ce maharan sun yi kokarin kwashe dalibai da dama amma hakan bai yiwu musu ba ” saboda a daidai suna kokarin haka ‘yan sanda suka far musu aka yi ta aman wuta babu kakkautawa a tsakanin jami’an mu da maharan.

A wajen su gudu ne suka arce da dalibai hudu.

A karshe rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar wa mutane cewa jami’an ta sun fantsama domin cafko wadanda suka aikata wannan mummunar abu.

Sannan kuma ya yi kira ga jama’a da su taimaka wa ‘yan sanda wajen sanar da su bayanan da zai rika taimaka musu wajen kama irin wadannan bata gari.

Idan ba a manta an yi garkuwa da wasu daliban makarantar kwana dake wannan gari na Kakau a watannin baya.

Sai da yaran makarantar suka shafe makonni kusan hudu tsare a wajen masu garkuwan kafin aka sako su.

Share.

game da Author