Yadda mahara suka far wa garin Tawara suka kashe mutane 15

0

Garin Tawara na karamar hukumar Kogi ne, jihar Kogi.

Kamfanin dillancin Najeriya ya ruwaito cewa wasu gungun mahara dauke da muggan makamai sun far wa garin Tawari sunda suka rika bude wuta ta ko’ina.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kogi Williams Anya ya tabbatar da wannan hari inda yace an kashe mutane 15 a lissafin da suka yo zuwa yanzu.

Bayan kashe mutane da suka yi maharan sun babbake gidaje da dama a garin Tawari din.

Da yawa daga cikin mutanen gari. Sun arce da ga garin a lokacin da maharan suka kai wannan hari.

Wata da ta zanta da wakilin NAN ta bayyana cewa yan uwanta sun rika kiranta suna gayamata halin da suka shiga a lokacin da aka kawo musu wannan hari.

Sai dai kuma bayan haka a cikin fushi, gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya umarci kwamishinan Yan sandan jihar da ya gaggauta cafke wadanda suka aikata wannan mummunar hari.

Ya umarce shi da ya baza dakarun sa su fantsama domin bankado wadanda suka aikata wannan mummunar al’amari.

Ita ma dai jibar Kogi na daga cikin jihohin da suke fama da hare-haren yan ta’adda da yan bindiga.

Duk da cewa an yi kwanaki da dan dama ba a samu irin wannan hare-hare ba irin wanda aka yi a garin Tawari ya tada wa mutanen jihar hankali matuka.

Share.

game da Author