Shugaban jam’iyyar APC Adams Oshiomhole ya bayyana cewa hassadace da bakinciki ake yi masa ganin cewa ya yi abinda ba a taba yi ba a jam’iyyar APC da wsu suke ganin ba yadda suke so ba yayi.
Oshiomhole ya ce ” Idan kaga yara na jifa a itace to sun hango nunannen mangwaro ne. Ammma haka kawai ba za su rika jifar itacen kwakwan da ba shi da ‘ya’ya ba.” A dililin haka yasa ake cakalar sa ta ko-ina.
Kowa ya san yadda muka iske jam’iyyar APC a lokacin da aka zabe mu a 2018. Yanzu akwa rata da muka ba wadanda suka jagoranci wannan jam’iyya a baya.
” Ana rantsar da mu muku tunkari zaben Ekiti da ke hannun PDP. Yanzu gwamna Fayemi ne gwamna a jihar. haka muka yi wa sauran zabubbukan da muka yi.
” A zaben 2015, idan baku manta ba ratar da shugaba Buhari ya ba Goodluck Jonathan na jam’iyyar PDP kuri’u miliyan uku ne da wani abu. Amma a 2019, mun ba PDP ratar kuri’u sama da miliyan hudu ne.
” Bayan haka mun taka rawar gani matuka a wajen zaben shugabannin majalisar Tarayyya da na Dattawa. A baya kiri=kiri PDP ta dauke kujerar mataimakin shugaban majalisa muna gani babu yadda zamu saboda lalaci. Amma yanzu fa Kaf muna muke da kujerun duka.
Oshiomhole ya yi dannan kalami ne da ya ke mika rahotan ayyukan jam’iyyar tun bayan rantasr da ita da aka yi a 2018 ga kwamitin zartaswar jam’iyyar.