‘VAT’: An fara karbar harajin jiki-magayi daga ranar Litinin – Gwamnatin Tarayya

0

Daga ranar Litinin ce za fara karbar harajin jiki-magayi, wato VAT, wanda Gwamnatin Muhammadu Buhari ta kara daga kashi 5 zuwa kashi 7.5 daga wasu kayyayakin da ’yan Najeriya ke saye, sayarwa ko wasu huldodin kasuwancin da suka yi.

Babban Akawun Najeriya, Ahmed Idris ne ya bayyana ranar fara karbar harajin, kasancewa Shugaba Muhammadu Buhari ya saw a Dokar Kara Haraji Hannu a ranar Litinin da gabata.

Yayin da ya ke tattaunawa da manema labarai a ofishin sa, Idris ya yinkarin hasken cewa wannan sabuwar doka duk wasu kudaden da gwamnatin tarayya ta biya daga asusun ta, to za a fara cire kashi 7.5 na haraji nan take.

“ A tsarin gwamnati, ba za ka fara aiwatar da wani tsari ba, har sai an samar da dokar da ta bada umarnin yin haka tukunna.

“ Ranar Litinin da ta gabata Shugaban Kasa ya sa wa Dokar Karin Haraji hannu, daga kashi 5 zuwa 7.5. washegari Talata sai aka kawo min lissafin biyan wasu kudi na watan Disamba, amma sai na ga an cire kashi 5 bisa 100 na haraji kadai. Ni kuma na ce ba zai yiwu ba.

“Na ce musu su je su buga sabon lissafi, su cire kashi 7.5 bisa 100 ba kashi 5 na tsohuwar doka ka.

“Ita doka daga ranar da aka kafa ta, to ko da tsohon aikin da ka yi za a biya ka kudi, ka yi aikin ne kafin dokar, muddin za a biya ka bayan an kafa dokar, to da sabon lissafin doka za a biya ka.”

Tun ranar da Buhari ya sa wa dokar amincewa da karin mafi kankantar albashi zuwa naira 30,000, ya hori masu ruwa da tsaki su fito da hanyoyin samu kudaden shiga daga haraji, domin a rika amfani da kudaden wajen biyan karin albashi.

Ba a dade ba sai Ministar Harkokin Kudade, Zainab Ahmed ta bada sanarwar yin harin kashi 50 bisa na harajin jiki-magayi, wato ‘Value Added Tax’ (VAT).

Share.

game da Author