Gwamnan Jihar Nasarawa Abdullahi Sule ya bayyana cewa su tuntuni suka fara aiki da kungiyoyin sa-kai a jihar.
Gwamna Sule ya ce babu wani yanki da ke fadin jihar da babu irin wannan kungiyoyi na ‘yan banga domin samar da tsaro a jihar.
Ba ya ga haka ya kara da cewa lallai jihar za ta karfafa wa irin wadannan kungiyoyi karfi domin su rika samar da tsaro a fadin jihar.
Sannan kuma hakan zai taimaka wa jami’an tsaron jihar wajen aikin kakkabe batagari a fadin jihar.
Idan ba a manta ba gwamnonin yankin kudancin Najeriya sun kafa yan sandan tsaro na yankin jihohin yarbawa.
Sai dai jim kadan bayan haka, ministan shari’a Abubakar Malami ya gargadi gwamnonin da su dakatar da wannan shiri na su yana mai cewa ya saba wa dokar kasa.
Wasu daga cikin gwamnonin sun fito karara inda suka bayyana cewa sun yi daidai kan abin da suka yi na kafa rundunar tsaro domin yankin yarbawan.
Gwamnan jihar Ondo Akeredolu, ya soki wannan korafi na gwamnati cewa ba su saba wa dokar kasa ba, kuma ba za su dakata daga wannan abu da suka saka a gaba ba.
Haka kuma wasu daga cikin dattawan yankin yankin sun bayyana karara cewa ba za su janye daga wannan shiri ba. Cewa sun yi haka ne domin samar ya mutanen yankin su tsaro daga mahara.