TSANANIN KISHI: Rabi ta babbake kanta saboda mijinta Badamasi ya yi mata kishiya

0

Wata matan aure mai suna Rabi ta cinna wa kanta wuta saboda mijinta Mallam Badamasi ya kara aure.

Radiyon ‘Freedom’ ce ta ruwaito wannan labari ranar Laraba inda ta bayyana cewa Rabi da mijinta Badamasi mazaunan kwatas din Gayawa ne dake karamar hukumar Ungoggo a jihar Kano.

Rahoton ya kara da cewa Rabi ta aikata wannan mummunar abu ne a cikin dakinta domin nuna tsananin kishin kara auren da mijinta ya yi.

Salisu Safiyanu sirikin Rabi ya ce ya iske gawar Rabi kone kurmus kulle a cikin dakinta.

Ita kuwa Malama Mariya ta ce har yanzu a rikice take ganin yadda ‘yar uwarta Rabi ta babbake kanta saboda kishi.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano Abdullahi Kiyawa ya tabbatar da haka inda ya kara da cewa rundunar na kokarin samun karin bayanan abin da ya faru daga ofishinsu dake nan unguwan.

Idan ba a manta ba a watan Satumbar 2019, PREMIUM TIMES ta ruwaito labarin yadda Aisha ta cinna wa kanta wuta saboda saurayinta mai suna Umar bai iya biyan kudin sadakinta ba.

Aminu Muhammed da abin ya faru a idon sa kuma mai unguwar kauyen Albarkawa ya shaida wa manema labarai cewa Allah yasa akwai mutane kusa da inda Aisha ta aikata wannan mummunar abu sai suka yi maza-maza suka kawo mata dauki suka kashe wutar kafin ta rasu a lokacin.

Share.

game da Author