TIRKASHI: Wani limami ya auri namiji bai sani ba sai bayan makonni biyu a gidan aure

0

Wani limamin masallaci a kasar Uganda ya auri wani namiji a matsayin mace bai sani ba.

Shi dai wannan limami mai suna Mohammed Mutumba ya auri amaryarsa ne bayan sun dade suna soyayya. Ashe da namiji ya ke ta jigila bai sani ba.

Mutumba shine limamin masallacin Kyampisi Noor dake kauyen Katunga, Uganda.

Bayan sun yi aure matar ta sa sai ta rika yi masa karya cewa tana jinin al’ada da hakan yasa limamin bai kusance ta ba ya ci gaba da hakuri.

Ashe, Ashe dai wani ne mai suna Richard kuma namiji ya ke ta damfarar sa.

Tuni dai mahukuntar wannan masallaci suka dakarar da liman Mutumba bisa zargin ya auri namiji zuwa sai bayan an kammala yin bincike akai.

Shi wannan mutum da ya damfari liman Mutumba ya bayyana cewa da gangar ya aikata abin da yayi domin ya dam samu kudade ne daga hannun sa.

Yadda aka kama ‘Richard’ matar Mutumba

A lokacin da Mutumba ya ke hakurin zaman kadaici zuwa lokacin da amaryarsa za ta kammala kwanakin al’adar ta, ashe ta kan tsallaka makwabta ta na yi musu sace sacen kaya.

Ranar da dubun ta ya cika kuwa sai aka cafke ta adaidai ta tsallaka makwabta tana sata.

Daga nan ne fa aka sa wata mata ta bincike ta ko akwai wasu kaya da ta boye a jikinta.

Nan ne fa aka rika ciro tsummokara a kwankwason ta da maman ta. Kwatsam kuwa sai aka gano ashe namiji ne ba mace ba.

Ko da aka kira liman Mutumba sai ya shaida wa masu bincike cewa shi bai taba sanin matar sa ba mace bace namiji ne.

Ya ce sai da ya biya sadakin ta, ya kuma yi kayan aure duk ya aika gidansu. Sai dai dama bai taba neman ya kusance ta ba.

Ita ma ‘yar uwan sa da ya yi karyar wai shi mace ce, an yi awon gaba da ita. Sai dai ta tabbatar wa masu bincike cewa bata taba sanin dan uwan ta namiji bane cewa tun tuni a matsayin ma ce ta san shi.

Share.

game da Author