TAMBAYA: Hukuncin wanda ake bi bashin azumin bara har na bana ya zo bai rama ba? Tare da Imam Bello Mai-Iyali

0

TAMBAYA: Hukuncin wanda ake bi bashin azumin bara har na bana ya zo bai rama ba? Tare da Imam Bello Mai-Iyali

AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW.

Mutumin da ake bin shi azumin bara, kuma bai rama ba har na bana yazo, ya nada hukunci kamar haka:

1 – Mustahabbi ne gaggauta ramakon azumi ga dukk wanda ya sha azumi.

2 – Wajibi ne ramakon azumi ga dukk wanda ya sha azumi, idan kwanakin Ramadana mai zuwa su ka rage dai-dai adadin kwanakin da sha. Misali: wanda ya sha azumin kwana uku, bai rama ba, har Sha’aban din bana ya rage saura kwana uku kacal ya kare. To, wajibin sa ne ya rama su cikin waddannan kwanaki uku.

3 – Dukk wanda ya yi jinkirin ramakon azumi har wani Ramadana ya zagayo, ba tare da wani karbabben uzuri ba, kamar rashin lafiya, to, ya yi mummunan aiki, kuma ya saba umurnin Allah.

4 – Zai rama adadin kwanakin da ya sha, kuma zai ciyar da miskini a adadin wannan kwanakin.

Wanda ya yi sakaci, har ramadanan bana ya zo, bai rama ba, bai rama na bara ba, Dole ya rama azumin kuma dole ya ciyar da miskini.

Imam Malik, Imam Shafi da Imam Ahmad, da sauran mayan malaman duniya sun bada wannan fatawan riko da Hadisin Ibn Abbas wanda Darul Kudiniyyu ya ruwaito: “Wanda ya yi sakacin ramakon azumin Ramadana, har wani Ramadana ya za gayo bai rama abinda ya sha ba, to, ya rama kwanakin da ya sha kuma ya ciyar da miskini a ko wane yini”.

Hakika macen da take shayarwa, zata sha azumi idan tana jin tsoron zata tagayyara ko kuma dan da ta ke shayarwa zai tagayyara.

Mai shayarwan da ta sha azumi don tsoron tagayyar ta ko na danta. Dole ne ta rama azumin kuma dole ta ciyar da miskini, bisa fatawar manyan malamai.

Lallai Allah SWT ya fada a cikin Al-kur’ani cewa: Lallai yin azumi shi ne mafi alkhairi ga duk masu ikon yin azumin.

Allah shi ne mafi sani.

Share.

game da Author