Sakamakon binciken da ‘Africa Polling Institute’ tare da hadin guiwar EpiAFRIC suka yi, ya nuna cewa mafi yawan ‘yan Najeriya sun karkata cewa tabuwar hankali na da nasaba da ko asiri aka yi wa mutum ko kuma aljanu ne suka shafi mutum.
Bisa ga wadannan ra’ayoyi da bincike da aka yi an gano cewa da dama ba haka bane. Kawai matsalolin rayuwa ce da rashin lafiya Sannan kuma wasu ma, ta’ammali da muggan kwayoyi ne yakan sa su samu tabuwar hankali da sai a rika cewa wai anyi wa mutum asiri ko kuma jifa.
Likitoci sun bayyana cewa hauka kan kama mutum ne idan ya samu matsala da kwakwalwar sa. Damuwa ma kawai kan iya jirkita kwakwalwar mutum da zai iya samun matsala a kwakwalwar sa.
Mutane da dama na da yakinin cewa idan mutum ya fara maganganu ko kuma yawo tsirara a titi shine ya haukace, ba haka kawai bane ke nuna alamar tabuwar hankali, wasu lalurorin kan sa mutum ya samu tabuwar hankali haka kawai.
Wani likitan masu fama da tabuwar hankali, Aremu Saad ya bayyana cewa rashin sani na daga cikin dalilan da ya sa mutane ke jingina duk wani matsala da ya shafi hankalin mutum ga asiri ko jifa.
Ya kara da cewa bincike ya nuna akwai wasu da dama dake fama da lalurar tabuwar hankali da zasu iya warkewa idan aka duba su a asibiti.
” Kashi 20 bisa 100 na wadanda ke fama da lalurar tabuwar kwakwalwa zasu iya warkewa, amma saboda rashin sani da kuma biye wa camfe-camfen al’ada sai kawai ka ga mutum ya garzaya wuraren bokaye da malaman karya wai ayi masa magani, ko an jefesa ko kuma wai an yi masa asiri.
A dalilin wannan matsala da ake fama dashi, a cewar hukumar WHO, akan samu mutane hudu da haka kawai suna fadawa cikin matsalar jirkicewar kwakwalwa. WHO ta ce akwai akalla mutane miliyan 450 da ke fama da tabuwar hankali a fadin duniya.
Muhimmiyar hanyar da gwamnati za ta bi wajen kawo karshen wannan matsala kuwa shine idan ta maida hankali da kara kaimi wajen wayar da kan mutane game da abubuwan da za su rika nisanta da kuma yadda za su kare kasnsu daga samun matsalar kwakwalwa.
Sannan kuma da wayar musu da kai game da yanayin da za su ji a jikin su domin gaggauta garzayawa zuwa asibiti a duba su.
Ya kuma kamata a rika tunarwa mutane su san cewa sau da yawa ba asiri aka yi wa mutum ba ko kuma ace wai aljanu ne suka kama mutum, rashin lafiyar ce kawai ta kwakwalwa kan sa arika wasu abubuwa da basu da kan gado. ” Musamman shan kwayoyi, da fadawa cikin damuwa da tsananin rashin lafiya duk kan sa a samu tabuwar hankali.