TA YI AMAI TA LASHE: Mu ne muka harbo jirgin Ukraine – Iran

0

Bayan karyata rahotannin da aka rika yadawa cewa wai ita ce ta harbo jirgin kasar Ukraine, kasar Iran ta lashe aman ta.

Tun bayan fashewar jirgin daga sararin samaniya da ya hallaka duka mutanen dake ciki kasar Iran ta rika cewa ba ita bace ta harbo jirgin bayan jirgin ya tashi daga filin jirgin saman kasar.

” Yau ranar bakin ciki ne. Bayan bincike da rundunar sojin mu suka yi, an gano cewa makamai masu linzamin mu ne ya kakkabo jirgin Ukraine daga sararin samaniya. Wannan kuskure ne da Kasar Amurka ta sa muka yi. ” Inji ministan harkokin kasashen wajen Iran, Javad Zarif.

” Muna mika ta’aziyyar mu ga iyalan wadanda abu ya shafa sannan kuma da kasashen da mutanen su ke cikin wannan jirgi.

Jirgin Boeing 737-800 ya tashi daga filin jirgin sama na Imam Khomeni da misalin karfe 6:12 na safiyar Laraba cike makil da fasinsoji 176 tare da matuka.

Duka fasinsojin dake cikin jirgin sun mutu bayan mizal din Iran ta harbo jirgin daga sama.

A cikin jirgin akwai ‘yan asalin kasar Iran 82, sai kuma baki da ‘yan kasar Canada suka fi yawa a cikin jirgin. Akalla yan kasar 60 ne suka mutu, sai kuma ‘yan kasar Jamus, Birtaniya da ‘yan kasar Ukraine.

A tun farkon aukuwar wannan hari kasar Iran ta musanta cewa ba ita bace ta harbo wannan jirgin.

Sai daga baya kuma shugaban kasar Canada da sune bakin da suka fi hasarar rayuka a harin jirgin ya bayyana cewa sun samu tabbacin cewa kasar Iran ce ta harbo wannan jirgi.

Ya koka kan yadda kasar ce ta fi yawan baki da suka rasa rayukan su a harin.

Share.

game da Author