Sojoji sun kama dan jarida ‘saboda rahoton Boko Haram’

0

Sojojin Najeriya sun kama wakilin jaridar Daily Trust a Maiduguri, dangane da wani rahoton da ya buga a kan Boko Haram.

An kama Olatunji Omirin ranar Alhamis a cikin sakateriyar Kungiyar ‘Yan Jarida ta Jihar Barno, aka buga masa ankwa, tare da ingiza shi a cikin motar su, kirar Hilux, aka yi gaba da shi.

An garzaya da shi, ba a zame ko in aba sai cikin Barikin Maimalari, inda wani babban soja wanda shi ne Mataimakin Daraktan Leken Asiri ke jiran a kai masa dan jaridar.

Haka dai PREMIUM TIMES ta samu labari.

An tsare Omirin har zuwa 7 na dare, daga nan aka sake shi, bayan da sauran ‘yan jarida suka matsa wa sojojin lamba ta hanyar kin halartar wani taron da sojoji suka shirya yi a ranar da karfe 5 na yamma.

Sai dai kuma Kwamandan Yaki da Boko Haram na Operation Lafiya Dole, Olusegun Adeniyi, ya bayyana cewa bai ma san da llabarin kamun da aka yi wa dan jaridar ba.

Omirin ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa an tsare shi da ankwa a hannu har zuwa wani lokaci.

Dan jaridar ya ce an tsare shi ne dangane da wani rahoton da ya bayar na yawaitar dayya Boko Haram ke kai hare-hare a kan titin Kano zuwa Maiduguri.

Ya shaida wa jaridar nan cewa jami’an sojan da ya yi masa tambayoyi y ace manyan sub a su jin dadin yadda ya bada labarin hare-haren da Boko Haram ke kai wa, Sannan kuma ya nemi ya sanar da shi majiyar sa.

“Jami’in sojan nan ya ji haushin yadda sojojin da suka kama ni ba su kai ni wurin sa tare da wayar GSM di na ba.” Inji Omirin.

“Ya ce min sojoji ba su dadin rahoton da na buga a ranar 20 Ga Janairu ba. Sai na ce musu, to saboda wannan ne har za ku sa min ankwa?’ Daga nan sai ya ba ni hakuri. Ya ce yaran sa sun dan wuce-makadi-da-rawa.” Inji Omirin.

Ya kara da cewa abin da sojojin suka so su samu shi ne wayar sa. Amma da suka ga bai je da wayar ba, ballantana su binciki abin da ke cikin wayar, sannan kuma ‘yan jarida na ta matsa musu lamba, sai suka sake shi.

Dama cikin watan Janairu, 2019 sai da sojoji suka kama wakilin Daily Trust A Maiduguri, kuma suka kai farmaki hedikwatar Daily Trust da ke Abuja.

Share.

game da Author