Shehu Sani ya sake ragargazar EFCC a kan tsarewar da ta yi masa

0

Tsohon Sanata Shehu Sani, ya sake rubuta wa Hukumar EFCC takardar ragargaza, dangane da ci gaba da tsare shi da suke yi a kan zargin karbar kudi da sunan Shugaban EFCC, Ibrahim Magu.

Sani ya yi ikirarin cewa wanda ke zargin na sa, Sani Dauda (ASD Motors), ya hada baki da EFCC domin a shirya masa gadar-zare.

Ya ce “da gangar aka shirya bayanin da ASD ya yi wa EFCC, kirkirar bayanan da sharri aka yi, aka sunkake su wuri daya domin a bata masa suna.”

Haka dai jaridar Sahara Reporters ta buga a jiya Litinin.

Ya kara da cewa “Idan ‘yan-koren gwamnati, wato EFCC da kuma wanda ke zargin sa su na da hujja, ai sai su gabatar, kamar murya, bidiyo, cakin kudi, rubutaccen sharadi ko yarjejeniya, wadanda za su bayyana duniya ta gani.

Daga nan sai sani ya kara jaddada cewa duk kulle-kulle ne aka shirya masa.

An dai zargi Shehu Sani da laifin karbar dala 25,000 da sunan zai kai wa Shugaban EFCC, Magu.

Tsohon Sanatan dai ya karyata wannan zargi, kuma ko a makon da ya gabata, ya bayyana cewa gadar-zare ce aka shirya masa, ta hannun ASD Motors kawai, kuma ba zai rufta ciki ba.

PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda EFCC suka kama Sani, sannan kuma a ranar 2 Ga Janairu, suka garzaya kotu, inda suka samu sammacin iznin ci gaba da tsare shi har tsawon kwanaki 14.

A cikin sanarwar da kakakin sa Sulaiman Ahmed ya fitar a ranar Lahadi, ya ce EFCC sun kulle asusun bankin Sani, domin iyalan sa sun nemi cikar kudi a ciki, amma aka nuna EFCC ta kulle asusun.

Sai dai kuma EFCC ta ce tabbas Shehu Sani na da abin da kotu za ta iya tuhuma a kan sa, dangane da wannan asarkala.

Jama’a da daman a mamakin ci gaba da tsare Sani har tsawon kwanaki 14 da EFCC ta ke yi.

Sannan kuma wasu na tunanin cewa ya aka yi ba a kama wanda aka ce ya bayar da kudin ba, domin idan har ya bayar din, to shi ma ya aikata laifi.

Share.

game da Author