Ministan Sadarwa, Isa Fantami ya shawarci matasan Najariya su rika fifita neman kwarewa ga nakaltar fasahar sadarwar zamani fiye da gaganiyar neman yin kwas din digiri a jami’o’i.
Pantami ya yi wannan kira a Hadejia, cikin Jihar Jigawa, yayin da ya ke bude Cibiyar Sadarwar Fasahar Zamani.
Ministan ya ce matasan Najeriya sun a da nakaltar kirkire-kirkiren fasaha, don haka ya ce wannan ne dalilin da ya sa gwamnatin tarayya ta kafa cibiyoyin koyon fasahar zamani a fadin kasar nan.
Ya ce wadannan cibiyoyi za su wadatar da matasa samun damar kwarewa a fannonin fasahar zamani.
“Wannan ilmin fasahar sadarwar zamani ya ma fi digiri da wasu satifiket muhimmanci ga matasa. Idan dalibi ya samu kwarewar fasahar zamani, sannan ya samu satifiket ya hada biyu, to hakan ya fi muhimmanci a gare shi.” Inji Pantami.
Minista ya ce inganta tattalin arziki ta hantar fasahar zamani magana ce ta samun kwarewar hoto, maimakon na samun kwalin satifiket din digiri.
Daga nan sai ya buga misali da wanda ya kirkiro Amazon, wato Jeff Bezos, wanda a yanzu ya wuce Bill Gates kudi a duniya.
Jeff Bezos inji Pantami a yanzu shi ne ya fi kudi a duniya, kima shekara uku kenan a jere babu wanda ya kai shi kudi a duniya.
An dai fara kafa wadannan cibiyoyi na gwaji a jihohin Bauchi, jigawa da kuma Rivers.
Gwamnan Jihar Jigawa, wanda dan kasuwa ne kafin shigar sa siyasa, ya ce kasuwanci da cinikayya sun fi saukin tafiyarwa ta hanyar samun kwarewa da ilmin fasahar sadarwar zamani.
Badaru ya jinjina wa Minsita Pantami da Gwamnatin Tarayya dangane da kirkiro wannan muhimmin shiri wanda zai kara ceto dimbin matasa daga matsalar rashin aikin dogaro a cikin kasar nan.
Sannan Badaru ya ce gwamnatin jihar Jigawa za ta bai wa shirin kwakkwaran goyon baya yadda zai samu nasara a Jigawa.