SHARI’AR KANO: PDP ta roki magoya bayan ta su zauna lafiya

0

Jam’iyyar PDP reshen jihar Kano ta yi kira ga magoya bayan ta da su zauna lafiya kada su tayar da fitina.

Wannan kira ya fito ne daga bakin Shugaban Riko Rabi’u Suleiman Bichi.

Suleiman ya yi wannan kira ne bayan da Kotun Koli ta bayyana kayar da dan takarar PDP, Abba Yusuf, tare da jaddada nasarar Gwamna Abdullahi Ganduje.

Ya kuma yi kira da su guji aikata wasu laifukan duk da za su kauce wa shari’a a jiha da kasa baki daya.

“Yanzu abin da ke gaban mu shi ne mu kara hada kan mu domin mu ciyar da jam’iyyar mu, PDP a gaba.

Ya ce PDP ta amshi hukuncin da Kotun Koli ta yanke.

Sai dai kuma shi dan takarar PDP Abba Yusuf, ya bayyana cewa an yi masa fashi a Kotun Koli.

‘Kotun Koli Ta Yi Wa PDP Fashi Da Rana Tsaka’ –Abba Gida-gida

A na ta raddin, jam’iyyar PDP ta bayyana hukuncin da alkalan Kotun Koli su bakwai a karkashin Cif Jojin Najeriya, Tanko Muhammad suka yi cewa fashi da makami ne suka yi wa jam’iyyar PDP a jihar Kano.

Sanusi Dawakin Tofa ya bayyana cewa, “A yanzu dai mun ga irin tsiyar da duk za su iya tabkawa, kuma sun tabka din.

Shari’a kuma sai a lahira a gaban Allah. Wannan ranar kuwa za a yi musu hukuncin ba za su iya tsallakewa ba.”

PRMIUM TIMES ta lura da cewa an jibge sojoji, ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro a manyan titinan birnin Kano da cikin birni, gudun ko da yamutsi ka barke.

Share.

game da Author