SHARI’AR IMO: Dalilai 5 da ya sa shugabannin PDP suka yi zanga-zanga a Abuja – Secondus

0

Shugabannin Jam’iyyar PDP na Kasa, a karkashin jagorancin shugaban jam’iyyar Uche Secondus, sun yi zanga-zangar lumana, domin nuna rashin goyon baya kan hukuncin da Kotun Koli ta yanke kan zabe Gwamnan Jihar Imo.

Cikin makon jiya ne dai Kotun Koli ta tsige tsohon gwamna Emeka Ihedioha na PDP, ta maye gurbin sa da wanda ya zo na hudu, Hope Uzodinma na APC.

Baya ga Secondus, wasu da suka shiga cikin jerin gwanon zanga-zangar sun dan takarar mataimakin shugaban kasa na PDP a lokacin zaben shugaban kasa, Peter Obi.

Mambobin jam’iyyar PDP daga jihohin Imo, Taraba, Yobe da Ogun duk sun yi zanga-zanga ranar Lahadi, inda su ma suk kira Kotun Koli ta gaggauta maida wa Ihedioka na PDP kujerar da suka kotu ta yi masa fashi da karfin tsiya ta kwace.

Wadanda suka yi zanga-zanga a Owerri, babban birnin jihar Imo dai sun datse manyan titinan birnin, suna rera wakokin tofin Allah-tsine ga hukuncin da Kotun Koli ta yanke.

A zanga-zangar uwar jam’iyyar PDP da aka gudanar yau a Abuja, masu zanga-zangar su na sanye da bakaken kaya, inda suka fara tattaki daga ginin ‘Legacy House’, inda can ne hedikwatar kamfen din PDP ta ke a cikin unguwar Maitama.

Daga nan suka darkaki Kotun Koli.

A ranar Juma’a, PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin taron manema labarai da Secondus ya kira, inda ya bayyana Cif Jojin Najeriya Muhammad Tanko da ‘farin-kare’ ne cikin tumaki, sannan ya nemi ya gaggauta maida wa Ihedioha kujerar sa.

Shugaban Jam’iyyar PDP, Uche Secondus, ya kira taron manema labarai na duniya, dangare da sakamakon shari’ar zaben gwamnan jihar Imo, wanda aka kwace daga gwamnan PDP aka bai wa dan takarar jam’iyyar APC.

Nan take jam’iyyar PDP ta nemi a gaggauta soke hukuncin da Kotun Koli a karkashin Cif Jojin Najeriya ta yanke, a maida wa gwamnan da aka tsige, Emeka Ihidioha kujerar sa.

Da ya ke magana a hedikwatar PDP, Uche Secondus ya ce yin haka ne kadai adalci dangane da wannann fashin mulki da Kotun Koli ta yi wa PDP da rana tsaka.

A zabe dai Uche Secondus na APC ya zo na hudu, amma shari’a da yake an ce sabanin hankali ce, sai Kotun Koli ta kwace daga hannun PDP ta bai wa Hope Uzodinma na APC.

Dukkan alkalai bakwai na kotun ne suka amince da haka, a karkashin Cif Jojin Najeriya, Tanko Muhammad, a ranar LLitinin da ta gabata, a Abuja.

Shari’a Sabanin Hankali

Secondus ya ce a karkashin shugabancin Tanko Muhammad Kotun Koli ta zubar da kimar ta, babu wata sauran martaba da daraja a kotun, domin Tanko ya damalmala mata lissafi, ya koma ya na kafa wata ajanda ta jam’iyyar APC mai mulki.

“Ai rainin hankali ne ma da kokarin haifar da tarzoma, a ce a kwace mulkin jihar daga hannun mai kuri’u 276,404, a damka ga wanda ya samu kuri’u 96,458, ta hanyar kirkiro wasu kuri’u na gangan, na bogi a dumbuza masa don kawai ana so a damka mulki a hanun sa. To mu ba za mu yarda da wannan rainin wayau din ba.”

“Wannan hukunci da Kotun Koli ta yanke, fashi ne, kuma juyin mulki ne aka yi wa PDP a jihar Imo da ma ’yan Najeriya gaba daya. Don haka bai kamata irin wannan rashin kunyar a bari ta samu wurin zama a karkashin mulkin dimokradiyya ba.”

Tambayoyin Da Secondus Ke So Tanko Ya Amsa

1. Shaidu nawa Uzodinma da APC suka gabatar daga rumfuna 388 din da Kotun Koli ta kamfato kuri’u ta dankara wa masa?

2. Kotun Daukaka Kara da Kotun Sauraren Kararrakin Zabe duk sun yi fatali da tulin katin kuri’un da aka gabatar musu. Ba su ma bude bugunan Ghana Must Go din takardun ba, domin sun ce babu bukatar yin haka. Abin mamaki ne yaushe Kotun Koli ta bude buhunnan har ta kidaya kuri’un da ta kara wa Uzodinma?

3. INEC ta bayar da dalilan da ya sa ba ta gabatar da sakamakon zabukan rumfukan 388 ba.

4. Da yawan wasu rumfunan daga cikin 388 ba a ma yi zabe a wuraren ba. To ina Kotun Koli ta samu yawan kuri’un da ta zabga wa Uzodinma na APC?

Ya aka yi sauran ’yan takara duk bas u ma san yawan kuri’un da suka samu a rumfuna 388 ba, sai APC kadai?

Cikin hujjojin da PDP ta kara bayyanawa, har da mamakin yadda aka yi APC da ta kasa cin ko da kujerar majalisar dokoki daya daga cikin kananan hukumomi 27, a ce kuma ta zarce PDP yawan kuri’u a abin da Secondus ya kira makahon hukuncin Kotun Koli a karkashin shugabancin Tanko Muhammad.

Share.

game da Author