Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana cewa an samu rudani da hargitsa zabuka da gangan a mazabu hudu.
INEC ta ce mazabun da aka yi yamutsin sun hada Oru ta Gabas/Orsu/Orlu da ke cikin Jihar Imo, Karamar Hukumar Essien da ke Jihar Cross River da kuma Karamar Hukumar Isa cikin Jihar Sokoto.
A ranar Asabar ne dai aka gudanar da zabuka a mazabu 28 a jihohi 11 da suka hada da Akwa Ibom, Bauchi, Benuwai, Cross River, Imo, Kaduna, Kano, Neja, Ogun da kuma Sokoto.
INEC ta ce sake zabukan ya bijiro ne bayan da aka samu korafe-korafe har guda 30 bayan kammala zabukan 2019.
Idan ba a manta ba, a ranr Litinin da ta gabata ne PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda INEC ta yi tir da yawan tashe-tashen hankulan da aka yi a Karamar Hukumar Essien Udim da ke Jihar Akwa Ibom.
Hukunci
Amma a ranar Talata ne Kwamishinan Zabe na Kasa, Festus Okoye ya fitar da wata takarda da ya sa wa hannu cewa INEC ta soke zaben Karamar Hukuma a Akwa Ibom, saboda marin da aka kai wa jami’an zabe a Jihar Akwa Ibom.
Har iya yau ta ce duk da cewa an samu tangarda a wasu wurare a jihohin Sokoto da Akwa Ibom da Cross River, an bayyana zaben ne saboda rigingimun da suka tashi ba su da wani tasiri a kan alkaluman yawan kuri’un da kowane dan takara ya samu.