A sake zabe da aka yi a wasu rumfunar zabe a wasu jihohin Kasar nan, manyan jam’iyyun kasar guda biyu sun taka rawar gani matuka.
A jihar Kaduna, Nuhu Goro na jam’iyyar APC ne ya lashe zaben kujerar majalisa na yankin karamar hukumar Sanga.
Goro ya doke Morondia Tanko na jam’iyyar PDP a zaben.
Goro ya samu kuri’u 24, 658, Morondia Tanko kuma kuri’u 20,206.
A Gwantu kuma, Comfort Amwe ce ta jam’iyyar PDP ta doke Halliru Gambo na APC.
A jihar Ogun, jam’iyyar APC ce ta yi nasara a zaben mazabar Ijebu-Ode.
A jihar Cross Rivers jam’iyyar APC ce ta yi nasara a zaben kujerar majalisar tarayya da aka yi.
Alex Egbonna na APC ya dome John Lebo na PDP a zaben kamar yadda malamin zabe ya bayyana a jihar ranar Asabar.
A jihar Bauchi kuma, PDP ce ta lashe zabukan da aka sake kad a jihar.
Sai dai kuma zabukan jihar Kano sun dan sha bam-bam domin kuwa an yi zaton dan majalisa Abdulmumini Jibrin zai kawo kujerar sa, amma kash hakan bai tabbata ba domin dan takarar PDP ya lallasa shi.
Ado Doguwa dake wakiltar yankin Tudun Wada da Doguwa a majalisar Tarayya ya lashe nasa zaben.
Ado Doguwa shine shugaban masu rinjaye na majalisar Tarayya.
Discussion about this post