Barcelona ta kori Ernesto Valverde a farkon makon da ya wuce, ta maye gurbin sa da Quique Setien, wanda aka dauko a daidai lokacin da ya bar Real Betis, ya koma kauyen su, ya na kiwon shanu.
A bisa dukkan alamu, idan Setien bai canja taku ba, to nan ba da dadewa ba ungulu za ta koma gidan ta na tsamiya, wato ya koma kiwon shanun sa.
Ci 2:0 din da Valencia ta yi wa Barcelona a ranar Asabar ya nuna cewa salon takun wasan da Setien ya fara koyar da Barcelona, ba zai kai su gaci ba. Barcelona ta sha kashi da ci 2, amma duk wanda ya kalli wasan ya san ta auna arziki da ba a sheka mata kwallaye 6 a raga ba.
Kwallon farko da aka ci Barcelona, ta bugi dan wasan ta ne Jordi Alba ta shiga raga. Wannan ne karo na 4 a baya-bayan nan da Alba ya jefa kwallo a kungiyar sa, Barcelona. Kuma shi ne dan wasan da ya fi kowa jefa kwallo a gida, a tarihin kafa Barcelona.
Lokacin da Barcelona ta dauko Valverde, sai da ya jera wasanni 29 ba a yi nasara kan kungiyar ba. Daga nan ne Espanyol ta yi nasara a kan Barca.
Shi kuwa Setien, wasan sa ba farko 2:1 ya ci, kuma bai yi armashi ba. Wasa na biyu a wannan makon, da wata karamar kungiya ce a gasar Copa Del Rey. An fara jefa wa Barcelona kwallo a raga, amma sai da aka yi awa daya cur su na kokarin ramawa su kara, abin ya faskara. Sai daga baya Antone Greizman ya samu ya ci kwallaye biyu.
Wasa na uku shi ne wannan, wanda Barcelona ta sha kashi, duk kuwa da cewa ta taka wa kociyan irin wasan da ya ke sha’awar su rika takawa.
Barcelona ta yi tabe-tabe sau 867, wannan ya karba ya tura wa wancan. Sai ga shi Valencia da ta yi tabe-tabe sau 298 kacal har aka tashi wasan, ta sheka mata kwallaye biyu. Don ma alkalin wasa ya hana wani ci da Valencia ta yi.
Bai kamata Barcelona ta sha kashi a hannun Valencia ba, kungiyar da ta buga La Liga cikin kwanakin nan amma ba ta yi nasara ba. Wasan ta kafin haduwa da Barcelona, kashi ta sha a hannun Mallorca, kungiyar da can kusa da ta karshe.
Mai tsaron gidan Barcelona, Marc-Andre ter Stegen ya yi kokari, ba don haka ba, sai an kwarara wa Barcelona kwallaye shida. Ya bige bugun daga kai sai mai tsaron gida, bayan Gerard Pique ya kayar da Jose Gaya. Kuma wannan ne fenaliti na farko da Ter Stegen ya taba bigewa a wasan La Liga.
Valencia ta yi nasara a kan Barcelona, alhali fitattun ‘yan wasan ta duk sun ji ciwo, ba su buga ba. Dani Pajero, Rodrigo, Denis Cherestev, Jesper Cillession, Gonzalo Guedes da Cristiano Paccini duk sun ji ciwo, ba su buga ba.
Lionel Messi ya yi kokarin cin kwallaye, amma bai yi nasara ba. Ya auna kwarewar sa har sau 11, amma kwallo ba ta shiga. Kuma wannan karo na farko da Messi ya auna raga sau 11 a wasa daya, ba tare da ya jefa kwallo ko sau daya ba.
Mai tsaron gidan Barcelona, Ter Stegen ya tare zafafan kwallaye 6 a cikin mintina 31 kacal. Wannan ne karon farko da wata kungiya ta yi wa Barcelona irin wannan rubdugun hare-hare a tarihin wasan La Liga.
Wannan sabon kociya dai a tarihi bai taba cin kofi ko da na modar shan ruwa ba. Wasu za su iya cewa ya na bukatar lokaci kafin ya yunkuro ya rika ragargazar manya da kananan kungiyoyi.
Sai dai kuma ko shakka babu, ita Barcelona ba ta da wannan isasshen lokaci da za ta ba shi.
Wasan Barcelona biyu na gaba, daya La Liga daya kuma Champions League su da Napoli, su kadai ne lokutan da za a iya ganewa shin Setien zai ci gaba da zama a Barcelona, ko kuwa zai yi gaggawar komawa kauye ne ya ci gaba da kiwon shanun sa?
Discussion about this post