Wani tsohon masanin dabarun haihuwar dabbobi, mai suna Sylvester Ibe, ya yi tir da yadda ya ke kallo a yanzu jami’o’in kasar nan ke rubdugun yaye dimbin dalibai ake cewa sun samu Digiri Mai Daraja ta Daya, wato First Class.
A wata tattaunawa da aka yi da shi, Ibe wanda ya yi ritaya kwanan nan daga koyarwa a Jami’ar Michael Okpara da ke Umudike, jihar Abia, ya bayyana cewa wannan rubdugun abin kunya ne ga jami’o’in kasar nan da ma tsarin ilmi baki daya a Najeriya.
Farfesa Ibe ya ce ya na mamakin yadda ake samun yawan dalibai a wannan zamani da suka samu digiri mai daraja ta daya, wato First Class, duk kuwa da cewa ana fama da karancin malaman jami’o’in kwararru a Najeriya.
Ibe, wanda ya shafe shekaru 47 ya na koyarwa a jami’o’i daban-daban, ya buga misali da wata jami’a mai zaman kan ta, wadda ya ce a bana ta yaye dalibai 1,580, amma abin mamaki a cikin su guda 215 aka ce sun samu ‘First Class’.
Ya ce hakan ya na nufin kashi 13.6 bisa 100 na daliban sun samu ‘First Class’ kenan.
Ibe ya ce a shekarun 1970 har zuwa bayqn 1980 kuwa duk abin ba haka ya ke ba, duk kuwa da cewa daga wancan lokacin ne aka fara samun bullar laifuka a jami’o’u da suka hada da kuniyoyin asiri, satar jarabawa, lalata da dalibai mata ana ba su maki da kuma illar yadda wasu baragurbin malamai ke rubuta wa dalibai kundin kammala digirin farko.
Daga nan sai ya yi kira ga gwamnati ta gaggauta shawo kan wannan gagarimar matsala, wadda ya ce ta kusa karasa zuwar da sauran kima da martabar da tsarin ilmi ke da shi a kasar nan.