RAHOTON MUSAMMAN: Yadda zafin muntsinin cirar harajin naira 50 a na’urar POS ke kawo mana cikas a sana’ar mu

0

Na’urar Cirar Kudi wato POS, wadda a yanzu ta zama ruwan dare da bankuna ke bai wa wasu ana kasuwanci cira ko tura kudade a asusun banki, ta zama tamkar zuma, wato ga zaki, sannan kuma ga harbi.

Zakin ta shi ne yadda cikin kankanen lokaci za ka yi hada-hadar aikawa ko cire kudi ba tare da ka je banki bin layin cire kudi ba.

Sai dai kuma zafin harbin shi ne duk lokacin da ka yi aike ko cikrar kudi sau daya, sai an ciri naira 50.

To maganar gaskiya dai kam wannan tsari da aka shigo da shi kwanan baya na cirar naira 50 daga asusun ajiyar mutum, ya na shafar harkokin talakawa manoma da ke zaune lunguna daban-daban, ciki kuwa har da na garin Luvu da ke cikin Jihar Nasarawa.

Daga daga cikin mai wannan sana’a ta kasuwancin cira da aika kudi ta POS, mai suna Jane David, ta bayyana wa wakilin PREMIUM TIMES da ya same ta Luvu cewa, “Gaskiya masu yin irnin wannan sana’a sai rufewa suke yi, saboda mutane sun daina sha’awar zuwa su ciri kudi ko su aika ta wurin mu, saboda cajin da aka dora a yanzu.

“Da yawan su sun fi ganin ai gara su je Maraba ko Area One a Abuja domin su ciri kudin su idan sun shiga gari kawai.” Inji ta.
Garin Luvu ya na cikin Karamar Hukumar Karu, a Jihar Nasarawa, amma kuma ya fi kusa da Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Ta ce akwai masu yin hada-hadar kudi ta POS a Luvu za su kai mutane 50 akalla. Sai dai kuma ta ce amma duk rabin su sun kulle, sun daina sana’ar.

Jane ta ce tun da gwamnati ta kara harajin naira 50 na cirar kudade a POS, a cikin Satumba, 2019, sai jama’a suka daina turururwar zuwa hada-hada a wurin su.

“ Kafin a yi karin dai mu na karbar naira 100 zuwa naira 150 a duk hada-hadar naira 5000, amma yanzu naira 200 muke karba, saboda shi ma POS din akwai na sa cajin.”

Wannan karin kudi naira 50 da Babban Bankin Najeriya, CBN ya yi, ya kawo cikas kwarai da gaske.

Karin abin haushi a cewar Janar, shi ne yadda ta ke neman yin biyu-babu, domin a da koyarwa ta ke yi. Da ta ga harkar POS ta na garawa, sai ta saki Koyarwa.

Amma yanzu da harkar ta za baya, ta fara fargaba sosai da sosai, kamar yadda ta shaida wa wakilinmu.

“Karin matsaloli shi ne ba bashi banki zai ba ka ba, sai dai ka sa kudin ka mai yawa, amma riba kadan. Kuma wani lokaci kudin da ka tut-tura, sai bayan awa 24 sannan zai je ko kuma ya shigo maka.

“A duk ranar Juma’a, masu POS na bankuna cikin fargaba suke, domin hada-hadar da suka yi a ranar ba zai shiga ba sai ranar Litinin.
“Amma kuma masu POS na kamfanoni, kamar OPay, su kudin su sha-yanzu-magani-yanzu ne.”

Irin korafin David Jane, iri daya ne da na Amos Ufmon da ke Kuje, wanda shi ma harkar hada-hadar kudi ta POS ya ke yi.
Ya ce da yawa sai mutum ya ci bashi kafin ya fara harkar.

“Sannan kuma banki ba zai baka POS ba sai ka ajiye naira 200,000 a bankin, cikin asusun da babu riba.

Wani ajan din na POS a jihar Nasarawa ya ce idan kasuwa ta yin kyau mutum kan samu naira 2,000 a rana daya.

Idan ba a manta ba, kididdigar Hukumar NIBSS ta nuna cewa cikin 2017 an yi hada-hada har sau milyan 146.3 ta zunzurutun kudade har naira tirilyan 1.4. Cikin 2018 kuma an yi sau milyan 285.9, ta kudi naira tirliyan 2.3. Tsakanin watan Janairu zuwa Yuni na 2019 kuma an yi hada-hadar naira tirilyan 1.4, wato sau milyan 187.7.

Karin Hadadar kudi a hannun masu Kananan karfi

Cikin 2010 ne Gwamnati ta fito da tsarin kokarin shigo da jama’a shiga tsarin hada-hadar kudi ta zamani, daga kashi 43.6 na wadanda ba su yi, aka so a rage zuwa kashi 20 bisa 100 kadai zuwa 2012.

Sai dai kuma kokarin da CBN ke yi mai nuna cewa daga mai karbar kudi kadai ba daga mai aikawa ba za a rika cirar kudin, har yanzu bai shiga kunnuwan mutane ba.

Domin PREMIUM TIMES ta yi bincike a Abuja, inda ta gano cewa dukn wata hada-hada da mutum zai yi a POS, ko ma wace iri ce, sai an cirar masa naira 50 sau ko sau nawa ya yi.

Wani masanin hada-hadar kudi mai suna Jide Ojo, ya bayyana cewa a bar ganin ana cirar wa mutane naira 50 a POS, kamar kudin kadan ne. Ya ce sai a yi la’akari da ko mutane milyan nawa ke amfani da POS a rana, to kudin da ake tarawa ne za su nuna cewa ana cirar kudade masu yawan gaske.

Shi dai babban bankin Najeriya, CBN na ganin cewa yin amfani da POS a karkara zai iya zaburar da jama’a da dama sha’awar bude asusun bankuna.

A jihar Jigawa an tattauna da wani mai suna Muhammadu Shekarau, a Karamar Hukumar Dutse, wanda ya ce a wajen su duk kuwa da ana hada-hada, kuma su na kusa da babban birnin jiha, har yanzu babu POS tukunna.

Mutane da yawa a Bauchi da Jigawa ma duk sun yi wannan korafi na rashin banki a kusa da su.

Share.

game da Author