PREMIUM TIMES ta kara samu cikakkun bayanan harin da Boko Haram suka kai wa wasu sojoji har suka kashe takwas tare da ji wa wasu rauni.
Al’amarin ya faru jiya Talata wajen karfe 1:00 na rana.
Dama kuma wannan jarida ta ruwaito yadda al’amarin ya faru a kauyen Mainok, kilomita 60 daga Maiduguri, babban birnin jihar Barno.
An hakkake cewa wannan farmaki aikin ’yan ta’addar ISWAP ne, wani bangare na Boko Haram.
Maharan sun yi shiga irin ta ’yan sanda kuma su na cikin motar ‘yan sanda. Sai da suka matsa kusa da sansanin sojojin, sai suka bude musu wuta, a wajen garin Mainok. Haka dai wata majiyar da ake ganin sahihiya ce ta bayyana.
Majiya daga cikin sojoji ta ce sai da aka shafe minti 30 ana bude wuta.
“ Sojojin na bayan ramin da suka giggina a wajen Mainok a lokacin da masu kai harin suka tunkari waurin. Kuma sun a cikin wata motar ‘yan sanda ce da suka kwata daga hannun ‘yan sanda.”
Haka wani jami’i ya bayyana, wanda a kan idon sa akafara budecwuta.
“Boko Haram sun yaudari kowa, saboda a cikin motar ‘yan sanda suka kai harin. Harin mai muni ne kwarai da gaske domin sun kashe sojoji bakwai kuma sun ji wa wasu rauni.
“A yanzu haka da na ke magana da kai, ba a san inda wasu sojojin suke ba. Ba a san irin halin da suke ciki ba.
Majiya ta ce an rasa inda sojoji biyu suka shiga bayan kai harin.
Rahotanni sun ce wajen karfe 1:00 na rana mayakan ISWAP suka darkaki wani ofishin ‘yan sanda, inda suka kwace wata motar su ta sintiri.
Dama kuma yau da rana PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda Boko Haram suka kashe wani babban jami’in sojan Najeriya da kuma wasu kananan sojoji bakwai, a wani harin kwanton-bauna da suka kai wa sojojin a lokacin da suke sintiri.
An kuma tabbatar da an jikkata wasu sojojin biyar, sannan kuma wasu biyu har yau ba a san inda suke ba, bayan al’amarin da ya afku jiya Talata.
Majiya ta kara da cewa an kashe dan Boko Haram daya, an kuma kwace bindigar da ke hannun sa.
An dai kai wa sojojin na Bataliya ta 156 hari misalin karfe 1:00 na rana a Mainok, wani kauye da ke nisan kilomita 60 tsakanin sa da Maiduguri.
Sojoji sun kwaso gawarwakin wadanda aka kashe, tare kuma da wadanda aka jikkata din.
An garzaya da wadanda suka ji rauni a wani asibitin sojoji kamar yadda majiyar PREMIUM TIMES ta tabbatar.
An kuma rasa inda aka yi da wasu motocin harba iggwa guda biyu da kuma makamin harbo jiragen yaki guda uku duk sun bace, an rasa inda suke bayan harin wanda Boko Haram suka kai wa sojoji.
An kasa tabbatar da shin Boko Haram ne suka yi awon-gaba da su, ko kuwa sojoji ne suka sauya musu mabuya.
Da safiyar yau PREMIUM TIMES ta kira kakakin sojojin Najeriya, Sagir Musa domin jin ta bakin sa, amma bai dauki waya ba.
Bayan sun yi shiru na wasu ‘yan makonni, yanzu kuma Boko Haram sun sake yunkurowa da karfin su cikin kwanakin nan.
Sun kara kaimi har ta kai su na ci gaba da kai hare-hare a kan fararen hula da tare babban titin shiga Maiduguri da ga Damaturu, wanda shi ne kadai hanyar da ake iya shiga babban birnin na jihar Barno.