Ra’ayin TY Danjuma bai fi na miliyoyin ‘yan Najeriya da suka sake zabe na ba – Buhari

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ra’ayin TY Danjuma ba shi da wani fifiko a kan ra’ayin milyoyin ‘yan Najeriya da suka sake zaben sa karo na biyu a shekarar da ta gabata.

Buhari ya yi wannan bayani ne cikin wata tattaunawa ta musamman da ya yi da Mujallar INTERVIEW, kuma aka watsa wasu bangarori na tattaunawar a ranar Asabar.

Shugaba Buhari ya amsa tambayoyin ne ta sakon i-mel, kamar yadda aka tura masa tambayoyin ta sakon i-mel.

Da aka tambaye shi wane raddi zai yi dangane da wani ra’ayi da TY Danjuma ya bayyana a wurin kaddamar da littafi a Ibadan, inda ya ce ya dawo rakiyar Buhari, domin ba zai iya kai kasar nan gaci ba.

Buhari ya amsa da cewa, “To kuma ya maganar milyoyin mutanen da ke biye da rakiya ta, wadanda suka sake zabe na? Ra’ayin su shi ne mafi muhimmanci a gare ni, ba ra’ayin mutum daya ba.”

Idan ba a manta ba, Danjuma wanda ya taba yin Babban Hafsan Hafsoshin Najeriya a zamanin mulkin soja, kuma ya yi Ministan Tsaro a zamanin mulkin dimokradiyya daga baya, ya ce, “da zan fallasa abin da na sani dangane da Buhari da gwamnatin sa, to babu wanda zai iya barci a kasar nan.”

Wannan kakkausar suka da Danjuma ya yi wa Buhari ta tayar da kura, ganin cewa ana kallon Danjuma daya daga cikin wadanda suka dauki nauyin kamfen din Buhari da makudan kudade

Sai dai Buhari ya ce sake zaben sa da jama’a suka yi alama ce da kuma hujjar cewa su na da yakini da kyakkayawan fata da zato a kan sa da kuma gwamnatin sa.

An tambaye shi ko yaya dangantaka ta ke tsakanin sa da Mataimakin sa, Yemi Osinbajo. Sai Buhari ya ce, “dangantakar mu na nan daram.”

Da aka matsa da tambayar ya bayyana irin yadda karfin dangantakar ta ke, sai Buhari ya nanata cewa, “ta na nan daram. Ko kuma shi Osinbajo din ne ya yi maka korafi?”

Wannan tattaunawa dai ba a nan ta tsaya ba. Buhari ya yi magana a kan zaben 2023 mai zuwa har ma akan ‘yan-ba-ni-na-iya da ake zargin sun kewaye shi, wato ‘cabals’.

Share.

game da Author