Gwamnatin tarayya za ta ciwo bashin dala miliyan 890 daga asusun duniya domin dakile yaduwar cututtuka a kasar nan.
Gwamnati ta ce za ta kashe wadannan kudade wajen yaki da cutar kanjamau, zazzabin cizon sauro da tarin fuka daga shekarar 2021 zuwa 2023.
Shugaban kwamitin sa ido kan tallafin da asusun duniya ke bai wa Najeriya (CCM) Dozie Ezechukwu ya sanar da haka da yake hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Abuja.
Ezechukwu ya ce bisa ga kason kudaden da gwamnati ta yi zazzabin cizon sauro zai dauki babban kaso daga cikin wadannan kudade da ya kai dala miliyan 417, kanjmau, dala miliyan 329 sannan tarin fuka dala miliyan 143.
Ya kara da cewa gwamnati ta tsara matakan da za su taimaka mata wajen kashe wadannan kudade yadda ya kamata ba tare da wani ko wasu sun yi sama da fadi da su ba.