Na fi karfin rubtawa gadar-zaren da wasu za su sa ASD ya gina min – Shehu Sani

0

Tsohon Sanata Shehu Sani ya bayyana zargin da EFCC ta yi masa na hannu wajen karbar dala 24,000 cewa kullalliya ce da kuma tuggu aka shirya masa domin a bata masa suna.

Da ya ke magana a ranar Juma’a, Sani ya ce “tuggu ne aka nemi shirya masa da kuma yunkurin rufe masa baki daga sukar gwamnati.

Ya ce wannan zargi kage ne, tuggu, sharri ne marar tushe da makama, kuma ba su da wata hujjar dora masa hakkin haihuwar yaron da ba shi ya yi cikin sa ba.

“Tsare ni da aka yi rashin adalci ne, rashin kuma makauniyar siyasa ce wadda ba za ta yi nasara wajen toshe min baki da tsumma don na daina magana ba.”

An dai zargi Sani da “karbar kudade daga hannun mai ASD Motors da nufin kai wa Shugaban Hukumar EFCC, Ibrahim Magu.”
A ranar 2 Ga Janairu ne EFCC ta samu umarnin kama Sani daga kotu.

Shi kuwa Chidi Odinkalu, ya bayyana cewa rashin adalci karara EFCC ta kama mutum akan zargi, sannan daga baya kuma ta garzaya kotu ta nemi a ba ta iznin ci gaba da tsare mutumin har tsawon kwanaki 14, wai da sunan bincike.

Sanata Sani, wanda rikakken mai adawa sa Gwamna El-Rufai ne, ya bayyana cewa, “shirya masa tuggu” ba zai iya toshe masa baki daga sukar wadanda ya ke suka ba.

“Kokarin da wasu tsiraru suka yi na watsa min dagwalon kashi a fuska domin na yi doyi, ba zai rage martaba da kima ta ba. ba kuma zai toshe min baki na yi shiru daga bayyana ra’ayi na ba.

Matsawar ina raye, to na fi karfin a yi amfani da wani karamin kwaro a toshe min baki.

“Na yi bayani a gaban EFCC kuma ina kalubalan tar su a fito da bayanan da kowa ya yi domin duniya ta gani.

“Alhaji Sani Dauda da abokan sharrin san a boye sun kasa gabatar wa EFCC shaidar zargin da suka yi mini. An tsare ni ba bisa ka’ida ba, kuma wannan rashin adalci ne, cuta ta aka yi. Zalunci ne.

“Wai su ne har da binciken gidana da kulle min asusun banki da kuma umarta ta na bayyana dukkan kadarorin da na mallaka. Wannan kuma tuni na riga na yi a ofishin da ya halasta a yi haka din, watau CCB.

Ya ce shi bai taba zama ya gana da Cif Jojin Najeriya ba, ballantana zama a kulla wani shirin karbar kudi tsakanin sa da Sani Dauda.

“Duk sharri ne da karairayi da tuggu da gadar-zare, aka yi amfani da Sani Dauda da EFCC domin a rubta ni na fada cikin rami.

“ASD karamin kwaro ne, ba shi ma da ilmin da zai iya shirya min gadar-zare, ballantana har na yi wawancin fadawa a ciki.”

Share.

game da Author