Sanatoci a majalisar Dattawa sun yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya gaggauta fatattakar shugabannin tsaron kasar nan cewa ya tabbata karara sun gaza.
A doguwar muhawara da aka yi a zauren majalisar ranar Laraba, Sanatocin sun bayyana cewa tsaro a kasar nan ya tabarbare matuka fiye da yadda yake a da.
A dalilin haka suka yi kira ga shugaban kasa da ya kori dukkan su ya nada wasu da za su yi wa kasa aiki.
Sanata Betty Afiafi, ta bayyana cewa babbar matsalar da ake fama da shi a kasar nan musamman a fannin tsaro a yanzu shine dadewar da shugabannin tsaron kasar suka yi. ” Basirar su ta kare, ya kamata a canja su kwata-kwata a kawo sabbin jini aga kokarin su.
Sannan kuma ta umarci sanatoci dake yawo da ‘yan sanda da maimakon haka su koma ofisoshin su domin su ci gaba da samar wa mutane tsaro a kasar nan.
Shi ko sanata Elisha Abbo, kira ya yi ga shugaban kasa da ya sake lale musamman a wajen maganar tsaro a kasar nan.
” Gaba daya basirar wadanda suke kai yanzu ta dode. Ba su da wata dabarar da ta rage musu. Shugaba Buhari ya gaggauta canja su kawai shine mafita.
” Ina so in tabbatar muku cewa Najeriya bata taba fadawa cikin halin kaka-ni-kayi na rashin tsaro ba irin a wannan lokaci. Tashin hankalin yayi yawa matuka.”
Sanata George Sekibo, kira yayi ga ‘yan Najeriya da kowa ya koma ga Allah. Ayi ta addu’oi. Ya ce hakan shine mafita yanzu.