1 – A raba beraye daga cikin gida: Kada a yi sakaci har beraye su samu wurin zama a cikin gida.
2 – A toshe duk wani rami a gida: Beraye daga wani gida kan shigo maka su boye, idan ka bar ramu a cikin gidan ka.
3 – A rika barin abinci ya dafu sosai: A rika cin abin da aka dafa ya dafu sosai.
4 – A guji taba mataccen bera ko mai rai da hannu: Taba mataccen bera ko mai rai da hannu na iya sa a kamu da cutar Zazabin Lassa.
5 – A rika yawaita tsaftace gida da kewayen sa: Barin datti a gina na kawo beraye ko daga waje ko daga wani gida.
6 – A guji cin kayan marmarin da bera ya gutsira: Wannan ganganci ne sosai, don haka a guji ci ko da kuwa an wanke.
7 – A rika ajiye abinci a wuri mai murfi: Bri abinci a bude kan kai bera ya ci, kuma har yay i fitsari ko kashi a kai.
8 – A rika rufe kwandon zuba shara: Beraye na buruntu cikin kwandon shara, su na cin sauran abincin da aka zubar.
9 – A rika wanke hannu da sabulu da ruwa mai tsafta: Dama wannan na cikin matakan farko na tabbatar da tsafta a jikin mutum.
10 – A rika garzayawa asibiti idan babu lafiya: Garzayawa asibiti ya fi a tsaya ana kame-kamen shan magani a gida.
11 – A daina shanya abinci a waje kuma a bude a kasa: Barin abinci a bude illa ce, sannan shanya abinci a kasa ko a kan dabe kan haifar da cututtuka.
12 – A guje kusantar wanda ya kamu da cutar: Likita ne kadai zai iya kusantar wanda ya kamu da zazzabin lassa. Don haka a kiyaye.

Discussion about this post